Ehlibeyt (as) Haber Ajansı ABNA - Tsohon firai ministan kasar Iraki Nuri Al-Maliki ya mayar wa jakadan kasar Amurka a Iraki da martani, dangane da wata wasika da aka mika masa da aka danganta ta da jakadan an Amurka.
A cikin wani bayani da ya rubuta a cikin shafinsa na twitter, tsohon firai ministan kasar Iraki kuma shugaban gungun siyasa na Daulat Qanun a Iraki Nuri Al-Maliki, ya bayyana cewa ya samu wani sako da aka danganta da jakadan Amurka a Iraki.
Al-Maliki ya ce idan sakon ba daga jakadan Amurka ya fito ba, to bai bukatar wani martani, idan kuma daga gare shi ya fito, to yanar da shi cewa, kasar Iraki kasa ce mai cikakken iko da ‘yancin siyasa, wadda ta ke yin aiki bisa maslahar al’ummarta ba wata kasar ketare ba, kuma ba za ta amince da shigar shugula ko shifta daga wata kasa ba, kuma batutuwa na cikin gidan Iraki, ba aikin jakadan wata kasa ba ne ya tsoma baki a cikinsu.
A cikin wasikar wadda aka aikewa Nuri Al-Almaliki da ake danganta tad a jakadan Amurka a Iraki, an bayyana cewa yana da kyau ku mara baya ga Mustafa Alkazimi domin kafa gwamnati, domin gwamnatin Adel Abdulmahdi babu abin da ta tabuka, idan kuka dafa aka kafa gwamnati to za mu ci gaba da taimaka ma Iraki.
Nuri Almaliki dai yana korafi kan yadda aka tsara mambobin majalisar ministoci da Alkazimi zai gabatar.
/129
6 Mayu 2020 - 08:17
Lambar labari: 1034053
Tsohon firai ministan kasar Iraki Nuri Al-Maliki ya mayar wa jakadan kasar Amurka a Iraki da martani, dangane da wata wasika da aka mika masa da aka danganta ta da jakadan an Amurka.