4 Mayu 2020 - 03:41
 Ministan Kwadago Na Nijar Mohamed Ben Omar Ya Rasu

Allah ya yi wa ministan kwadago na Jamhuriyar Nijar, Mohamed Ben Omar rasuwa a wannan Lahadi 3 ga watan Mayu, yana mai shekaru 55 a duniya.

(ABNA24.com) Allah ya yi wa ministan kwadago na Jamhuriyar Nijar, Mohamed Ben Omar rasuwa a wannan Lahadi 3 ga watan Mayu, yana mai shekaru 55 a duniya.

Mirigayin ya rasu ne a babban asibitin kwararu na Yamai babban birnin kasar, bayan 'yar gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda wata majiya daga Jam'iyarsa ta PSD-Bassira ta tabbatar wa gidan radiyo Hausa VOH.

Tuni dai shugaban kasar Mahammadu Isufu, ya aike da sakon ta'aziyya da iyalen mirigayin dama al'ummar kasar baki daya.



/129