25 Afirilu 2020 - 08:04
​Iran: Rauhani Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Shiga Watan Ramadan Ga Shugabannin Kasashen Musulmi

Shugaba Rauhani na Iran ya aike da sakon taya murnar shiga watan Ramadan mai alfarma zuwa takwarorinsa na kasashen musulmi.

(ABNA24.com) A cikin bayanin da ofishin shugaba Rauhani ya fitar a jiya Juma’a, an bayyana cewa shugaban kasar ta Iran ya aike da sakon taya murnar shiga watan Ramadan mai alfarma, zuwa ga dukkanin shugabanni na kasashen musulmi.

Shugaba Rauhani a cikin sakon nasa ya yi fatan alhairi ga dukkanin shugabannin kasashen musulmi da kuma al’ummomin kasashensu, tare da bayyana wannan lokaci na ibadar azumi da cewa lokaci ne mai matukar muhimmanci ga dukkanin musulmi, tare da bayyana shi a matsayin wata babbar dama ta yin addu’a da rokon Allah ya kawo karshen annobar corona a dukkanin kasashen musulmi da ma sauran kasashen duniya baki daya.

Haka nan kuma shugaba Rauhani ya yi fatan samun rahmar ubangiji da tausayinsa da gafararsa ga dukkanin al’ummar musulmi na duniya baki daya, da kuma samun dawawwamen zaman lafiya da ci gaba da kuma yarwatar arziki.


/129