21 Afirilu 2020 - 07:45
​Tunisia: An Tsawaita Zaman Gida Saboda Dakile Cutar Corona

Gwamnatin kasar Tunisia ta bada sanarwar tsawaita zaman gida a kasar har zuwa 4 ga watan Mayu mai kamawa a kokarinta na dakile cutar Corona.

(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Tunisia ta bada sanarwar tsawaita zaman gida a kasar har zuwa 4 ga watan Mayu mai kamawa a kokarinta na dakile cutar Corona.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto firai ministan kasar Elyas Fakhfakh yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa daga ranar 4 ga watan Mayu ne yake sa ran za’a fara bude harkokin kasuwanci a kasar mataki-mataki.

Rahoton ya kara da cewa masana suna hasashen cewa tattalin arzikin kasar ta Tunisia zai yi rauni a wannan shekara, kuma karfinsa zai ragu da kashi 4.3%. Sannan bangaren yawon shakatawa na kasar zai yi hasarar dalar Amurka biliyon 1.4 a yayin da ma’aikata 400,000 zasu rasa ayyukansu.

Ya zuwa yanzu dai mutane 866 ne aka tabbatar da kamuwarsu da cutar ta Corona a kasar, sannan 37 daga cikinsu sun rasa rayukansu.

Haka nan kuma rahoton ya kara da cewa, gwamnatin kasar ta shaida wa asusun lamuni na duniya IMF matsalolin tattalin arzikin da kasar za ta fuskanta sanadiyyar cutar da Corona.


/129