21 Afirilu 2020 - 07:41
​Syria: Jirgin Yakin Rasha Ya Kora Wani Jirgin Yakin Amurka A Yankin Hamimim

Rundunar sojin kasar rasha ta sanar da cewa, ta kora wani jirgin yakin Amurka da ya kutsa kai a cikin yankin Hamimim na kasar Syria.

(ABNA24.com) A cikin wani bayani da ta fitar a yau, ma;aikatar tsaron kasar Rasha ta bayyana cewa, jirgin yakin na Amurka ya taso daga kan babban jirgin rowan Amurka mai daukar jiragen yaki, wanda yake a cikin tekun Mediterranean, wanda kuma ya dumfaro yankin Latakia na kasar Syria, inda a nan sansanin sojin Rasha yake a yankin Hamimim.

Bayanin ya ce bayan da na’urorin sojojin Raha da suke sanya idoa sararin samaniyar Syria suka hango jirgin, wani jirgin yaki na Rasha ya tashi, kuma ya tilasta jirgin na Amurka komawa inda ya fito.

Ma’iaktar harkokin wajen Rasha ta bayyana cewa dakarunta suna girmama dukaknin yarjejeniyoyi na kasa da kasa dangane da ayyukan da suke gudanarwa a kasar Syria, amma kuma ba za su bari wani bangare ko wata kasa ta yi shishigi a kan dakarunsu da ke kasar Syria ba.


/129