(ABNA24.com) Ministan kiwon lafiya na Iran wanda ya gabatar da taron manema labaru ya bayyana cewa; Kowane rayin dan’adam yana da kima da daraja, amma a yau ita ce rana ta farko da adadin wadanda su ka mutu saboda corona bai wuce lambobin kididdiga kwaya biyu ba, wato 98.
Ministan kiwon lafiyar, Sa’id Namaki ya kara da cewa; Iran tana da kyakkyawan tsari na fada da cutar Covid-19, kuma a halin yanzu ana samun kyakkyawan sakamakon a cikin mafi yawancin gundumomin kasar.
Ministan kiwon lafiyar na Iran ya kara da cewa; Tsarin nisantar juna da ake amfani da shi a cikin al’umma yana ci gaba da aiki, kuma ana aiwatar da shi cikin yanayi mafi dacewa.
Ya zuwa yanzu dai adadin masu dauke da cutar “Corona” a Iran sun kai dubu 74 da dari 877,adadin wadanda kuma cutar ta kashe sun kai dubu 4 da dari 683.
./129
16 Afirilu 2020 - 04:59
Lambar labari: 1026283
Ministan kiwon lafiya na Iran wanda ya gabatar da taron manema labaru ya bayyana cewa; Kowane rayin dan’adam yana da kima da daraja, amma a yau ita ce rana ta farko da adadin wadanda su ka mutu saboda corona bai wuce lambobin kididdiga kwaya biyu ba, wato 98.