14 Afirilu 2020 - 05:53
Wani Likita Musulmi Ya Samar Da Na’urar Da Ke Taimakawa Wajen Lumfashi A Amurka

Wani likita musulmi a kasar Amurka ya samar da wata na’ura da ke taimaka ma masu fama da cutar corona wajen yin lumfashi.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na arabicpost cewa, mutanen Amurka sun jinjina wa likitan musulmi mai suna Dr. Saud Anwar, wanda ya samar da na’ura mai taimakawa wajen yin lumfashi, domin amfanin masu fama da matsalar corona.

Bayanin ya kara da cewa, Dr. Saud Anwar wanda ya yi karatu a jami’ar Karachi da ke kasar Pakistan, ya karanci likitanci kuma ya kware a bangaren kwada, daga bisani ya koma Amurka da zama baki daya, inda yake gudanar da aikinsa.

Bayan gargadin da gwamnan New York ya yi a kwanakin baya kan karancin na’urorin da suke taimakawa wajen lumfashi a asibitocin da ake kwanatar da masu fama da matsalar corona, Dr. Saud Anwar ya shiga gudanar da aikin samar da wata na’ura wadda za ta taimaka a wannan bangaren.

A halin yanzu na’urar da ya samar an fara aiki da ita wajen taimaka ma masu matsalar corona a kasar Amurka.




/129