5 Afirilu 2020 - 07:25
Iran Za ta Fara Amfani Da Shirin (IP) Don Gwajin Cutar Corona

Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan fara amfani da tsarin (IP) ko “Artificial Intelligence” don gano wadanda suka kamu da cutar Corona a kasar.

(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan fara amfani da tsarin (IP) ko “Artificial Intelligence” don gano wadanda suka kamu da cutar Corona a kasar.

Kamfanin dillancin labaran “Iran Press” ya nakalto mataimakin shugaban kasa kan kimiyya da fasaha a kasar Sorena Sattari yana fadar haka a jiya Asabar.

Sattari ya kara da cewa na’urorin IP sun fi bada sakamako mafi kyau a cikin karamin lokaci, idan an kwatanta da kayan gwaji na ( test kits ) wadanda ake amfani da su a mafi yawan kasashen duniya a halin yanzu.

Har’ila yau Sattari ya kara da cewa a halin yanzu dai ana amfani da kayan gwaji na (test kits) 100,000 a duk fadin kasar, amma an bada kwantiragin samar da wasu 250,000 a cikin gida.

Daga karshe mataimakin shugaban kasar ya ce ana yin gwaji kimanin 100,000 a kowace rana a cikin kasar. Sannan akwai kamfanonin da suka kere na’urar tallafawa numfashi wacce ake kira “Ventilators” a kasar.


/129