(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da hukumar maguguna ta kungiyar tarayyar turai ta fitar a jiya ta bayyana cewa, bisa la’akari da halin ake ciki da kuma sarkakiyar da take tattare da kwayoyin cutar corona, samar samar da maganin cutar da zai kawo karshenta a duniya, yana bukatar lokaci da ba zai gaza shekara guda ba a nan gaba.
Bayanin hukumar ya ce a halin yanzu akwai gwaje-gwaje da dama da aka yi, da kuma wadanda ake cikin yi na mugunguna daban-daban a kan cutar ta corona, kuma har yanzu ba a kai ga yanke matsaya ta karshe akan wani magani guda ba.
Hukumar ta ce bisa la’akari da masaniya da kuma gogewa da masana ilimin magunguna suke da ita, da kuma kokarin da ake yi a halin yanzu kan batun, za a samu nasarar samun maganin cutar wanda zai kawo karshenta, amma haka nan bukatar lokaci, wanda zai iya kaiwa nan da shekara guda mai zuwa.
342