31 Maris 2020 - 15:58
Kasar Rasha Ta karyata Shugaban Amurka Game Da Bukatar Cire Mata Takunkumi

Kakakin fadar Karmilin ya bayyana cewa kalaman da shugaban kasar Amurka ya yada na cewa shugaban kasar Rasha Biladin min Putin ya bukaci a dauke takunkumin da aka kakabawa kasarsa labari ne kawai na kanzon kurege ,

(ABNA24.com) Ana sa bangaren Demitry Pasfuk kakakin fadar shugaban kasar ta Rasha da yake amsa tambayoyin yan jaridu game da wannan batu ya fadi cewa: wannan kalaman da Donald Trumph ya yada ba shi da sihihanci ko kadan karyace kawai .

A wata hira da shugaban kasar Amurka Donald Trumph yayi da gidan talbijin din Fax News ya fadi cewa: a wata ttaunawa ta wayar tarho da zai yi da shugaban kasar rasha ya ce da da alama shugaban na rasha zai matsa lamba kan Amurka da ta janye takunkumi da ta kakabawa kasarsa,

Wannan ikirarin na Trumph yana zuwa ne a daidai lokacin da shugaban rasha Biladmin Putin ya sha jaddada cewa ba shi da wata aniya ta neman Amurka ta janye takunkumin da ta kakaba wa kasarsa.

342