30 Maris 2020 - 07:13
Iran : Kula Da Kiwon Lafiya Shi Ne Gwamnati Ta Sanya A Gaba

Shugaban kasar Iran, Dakta Hassan Rohani, ya bayyana cewa, kula da kiwon lafiyar al’umma shi ne gwamnatinsa ta sanya a gaba, a daidai wannan lokacin da kasar ke yaki da cutar coronavirus.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran, Dakta Hassan Rohani, ya bayyana cewa, kula da kiwon lafiyar al’umma shi ne gwamnatinsa ta sanya a gaba, a daidai wannan lokacin da kasar ke yaki da cutar coronavirus.

Dakta Ruhani, wanda ke bayyana hakan yau Lahadi, yayin wani taron masu ruwa da tsaki a ofishinsa, ya ce babu wani abu da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai yanzu, kamar kula da sha’nin kiwon lafiyar al’ummar kasar.

Kuma a cewarsa gwamnati za ta yi duk abunda ya tsawaka domin kare jami’an kiwon lafiya wadanda su ne ke sahun gaba wajen yaki da wannan annobar.

Shugaban kasar ya kuma sanar da cewa gwamnatin da kuma kamfanonin inshora na daukar yaunin kashi 90 cikin dari na kudin kula da masu fama da cutar ta coronavirus a kasar.

Alkalumman baya baya nan da ma’aikatar lafiya a Iran ta fitar sun nuna cewa mutum 38,309 ne suka kamu da cutar, sai kuma wasu sama da 2,640 da cutar ta yi ajalinsu, a yayin da adadin wadanda suka warke daga cutar ta covid-19 ya kai 12,391.




/129