(ABNA24.com) Sanarwar ta ci gaba da cewa; Shugaban kasar ya dauki wannan matakin ne bayan komawarsa gida daga halartar bikin rantsar da shugaban kasar Namibia, Hage Geingob a birnin Windhoek.
Wani sashe na sanarwar ya kuma ce; A daidai lokacin da shugaban ya ke killace za a rika yi masa gwajin cutar Corona, domin sanin halin da yake ciki,kuma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa daga gida, amma zai nesanci haduwa da iyalansa.
Bugu da kari,sanarwar ta bai wa ‘yan tawagar shugaban kasar da su ka kai ziyara zuwa Namibia da su dauki irin wannan matakin na killace kawukansu.
Daga cikin shugabannin kasashen Afirka da su ka halarci taron na rantsar da shugaban Namibia da akwai shugabannin kasashen Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da na Angola Joao Lourenco.