15 Maris 2020 - 06:44
Coronavirus : Ana Ci Gaba Rufe Makarantu Da Jami'o'i A Afrika

A Afrika an fara rufe makarantu da jami'o'i da kuma haramta taruruka a wani mataki na yaki da yaduwar cutar corona.

(ABNA24.com) Matakin baya baya nan shi ne na kasar Senegl, wacce ta sanar da rufe makarantu da jami’o’in kasar har na tsawon makwanni uku a wani mataki na yaki da yaduwar cutar coronavisrus a kasar.

Shugaban kasar ta Senegal, Macky Sall, ya sanar da rufe makarantu da jami’o’in kasar har na tsawon makwanni uku a wani mataki na yaki da yaduwar cutar coronavisrus a kasar.

Haka kuma shugaban ya dau matakin haramta duk wasu taruruka a fadin kasar har na tsawon kwanaki 30, ciki har da bukukuwan zagayowar ranar kasa ta 4 ga watan Afrilu mai zuwa.

Shugaban ya kuma za’a karfafa binciken kiwon lafiya a duk wani shige da fice a iyakokin kasar na sama da kasa da kuma na ruwa.

An kuma dakatar da duk wansu shirye shirye da suka shafi aikin hajji zuwa kasa mai tsarki da kuma na al’ummar kristoci.

Daukar wadannan matakan ya biyo bayan gano bullar cutar coronavirus dake yaduwa a yankin Touba inda aka gano mutum 11 dauke da cutar.

Tunda farko dama akwai mutane 22 dake jinyar cutar ta Covid-19 a kasar ta Senegal.

A kasashen Burkina Faso da Mauritaniya ma an sanar da rufe makarantu saboda barazanar cutar ta corona.


/129