(ABNA24.com) Sai dai shugaban na kasar Turkiya ya yi alkawalin ci gaba da kai farmaki a yankin na Idlib idan har sojojin Syria su ka keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki, kamar yadda ya fada.
Turkiya wacce ta aike da sojoji cikin kasar Syria tana fuskantar matsin lamba daga gwamnatin Damascuss da kawayenta. A cikin makwannin bayan nan dai sojojin Syria sun kai hare-hare akan sojojin na Turkiya tare da kashe adadi mai yawa nasu.
Gwamnatin ta Syria dai tana zargin Rajab Tayyib Urdugan da taimakawa kungiyoyin da su ke dauke da makamai na “Free Syrian Army” da kuma ‘yan ta’addar Jaish Tahriru-s-sham.
/129
Shugaban Kasar Turkiya Ya Yi Furuci Da Cewa Sojojin Kasarsa 59 Ne Aka Kashe A Yankin Idlib Na Kasar Syria
9 Maris 2020 - 10:50
News ID: 1015816
Shugaban na kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan ya kara da cewa; An kashe wadanan adadin sojojin ne a daga karshen watan Febrairu zuwa yanzu.