(ABNA24.com) Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce ko da taki guda kasarsa ba za ta janye daga yankin Idleb na Siriya ba, inda dakarun kasashen biyu ke gwabza fada lokaci zuwa loaci.
M. Erdogan ya bayyana a yau Laraba yayin wani jawabi cewa, ba zamu ja da baya ba, ko da da taki guda ne daga yankin na Idleb, dake arewa maso yammacin kasar ta Siriya, kuma zamu kora gwamnatin Siriya daga iyakokin da muka shata.
A baya bayan dai dakarun gwamnatin Siriya dana Turkiyya na gwabza fada a yankin na Idleb wanda gwamnatin Siriya dake samun taimakon sojojin Rasha ke kokarin kwacewa daga ‘yan tada kayar baya da kuma mayakan dake ikirari da sunan jihadi.
Kafin hakan dai a ranar 21 ga watan nan, M. Erdogan ya bayyana cewa, shugaban kasar Faransa da shugabar gwamnatin Jamus sun bada shawarar kiran taron kolin kasashen Rasha, Turkiyya, Faransa da Jamus kan batun na Siriya.
Bangarorin dai za su yi tattaunawa ne kan yankin Idlib na Syria, da kasar Turkiyya ke kokarin fadada ikon ta a ciki.
/129
27 Faburairu 2020 - 06:08
Lambar labari: 1013531
Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce ko da taki guda kasarsa ba za ta janye daga yankin Idleb na Siriya ba, inda dakarun kasashen biyu ke gwabza fada lokaci zuwa loaci.