24 Faburairu 2020 - 05:10
​Najeriya: Bankin Zenith Ya Samu Ribar Fiye Da Naira Biliyan 240 A Cikin 2019

Bankin Zenith ya bayyana cewa ya samu riba ta zunzurutun kudade har naira bilyan 208.8 a cikin 2019.

(ABNA24.com) Jaridar Premium Times ta bayar da rahoton cewa, a sanarwar da bankin ya fitar a karshen makon nan, ya bayyana cewa ya samu ribar naira bilyan 243 a cikin 2019, amma ribar ta koma bilyan 208.8, bayan cire harajin da ake biya ga gwamnati.

Wannan ne karo na farko a tarihin kafa harkokin hada-hadar bankuna a kasar, da aka samu riba a wani banki guda da ta haura naira bilyan 200.

A cikin 2018 dai Bankin Zenith ya samu ribar naira bilyan 232, bayan biyan haraji kuma kudin ribar ya rage saura naira bilyan 193.

Shugabannin bankin sun ce akalla Bankin Zenith ya na da kadarori da jari da jimillar adadin su ya kai naira tiriliyan 6.35.

Sun ce kadarori da jarin bankin ya karu idan aka kwatanta da yawan su a shekarar 2018, inda a lokacin yake da naira tiriliyan 5.96.

Daga nan sun yi sanarwar cewa za a raba ribar bankin a kan naira 2.80 ga kowane hannun jari daya.


/129