9 Faburairu 2020 - 10:35
​Wasu ‘Yan Majalisar Dattijan Amurka Sun Bukaci A Rufe Shafukan Ayatollah Khamenei Da Zarif A Twitter

Wasu daga cikin ‘yan majalisar dattijan kasar Amurka sun bukaci kamfanin twitter da ya rufe shafukan sadarwa na jagoran juyin juya halin muslucni na Iran da kuma ministan harkokin wajen kasar.

(ABNA24.com) Wasu daga cikin ‘yan majalisar dattijan kasar Amurka sun bukaci kamfanin twitter da ya rufe shafukan sadarwa na jagoran juyin juya halin muslucni na Iran da kuma ministan harkokin wajen kasar.

Tashar presstv ta bayar da rahoton cewa, a cikin sakon da sanatocin wadanda dukkaninsu ‘yan jam’iyyar Republican ne suka aike wa babban daraktan kamfanin na twitter, sun bayyana cewa dole ne ya rufe shafukan Ayatollah Khamenei da kuma na Muhammad Jawad Zarif, saboda rashin yin hakan ya saba wa takunkuman da Donald Trump ya dora musu.

Sakon nasu ya kara da cewa, jami’an Iran suna yin amfani da shafin twitter wajen bayyana mahangarsu ga duniya, wanda hakan ya saba wa dokokin Amurka, kuma dole ne kamfanin na twitter ya dauki matakin dakatar da hakan cikin gaggawa.

A ranar 24 ga watan Yunin shekarar 2019 da ta gabata ce, gwamnatin kasar Amurka bisa umarnin shugaban kasar Donald Trump ta sanar da kakaba takunkumi a kan jagoran juyin juya halin muslunci an Iran Ayatollah Khamenei, da kuma dakarun kare juyin juya halin muslunci na kasar.



/129