(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa Yusuf bin Alawi minstan harkokin wajen kasar Omman a kan hanyarsa ta komawa gida daga taron tattalin arziki na Davos ya ya da zango a birnin Tehran inda ya gana da Muhammad Jawad Zarif tokoransa na kasar Iran.
Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da suka shafi tsaro a yankin tekun farisa musamman a mashigar ruwa ta ya Hurmus. Kasashen biyu sun amince da aiki tare don min cimma wannan manufar.
Har’ila yau kasashen biyu sun tattauna batun tsaro a kan iyakokin kasashen biyu na ruwa.
Wannan dai shi ne haduwar ministocin harkokin wajen na kasashen biyu karo na 4 a wannan watan. Kafin haka a ranar tarlatan da ta gabata ma Yusuf bin Alawi ya gana da Zarif a birnin Tehran.
/129
27 Janairu 2020 - 06:51
Lambar labari: 1005815
Ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Oman sun gana a birnin Tehran a jiya Lahadi.