21 Janairu 2020 - 15:03
An Harba Rokoki 3 A Kusa Da Ofishin jakadancin Amurka Da Ke Iraki

Wasu rokoki da aka harba sun sauka a kusa da ofishin jakadancin kasar Amurka da ke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki.

Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA-ta rawaito Tashar almayadeen ta bayyana cewa a daren jiya an harba wasu makaman roka guda uku a kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Bagadaza na kasar Iraki, sai dai babu wasu bayanai kan barnar da hakan ya jawo.

Tun bayan kai da Amurka ta yi kwanakin baya a kan sansanonin dakarun sa kai na al’ummar kasar Iraki, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar 25 daga cikinsu, al’ummomin Iraki suka fara kai wa ofishin jakadancin kasar Amurka hari, wanda hakan yasa jakadan na Amurka ya arce daga wurin.

Bayan kisan Kasim Sulaini da Abu Mahdi Muhanddis mataimakin rundunar sojin sa kai na Iraki da Amurka ta yi, majalisar dokokin Iraki ta bukaci Amurka da ta fitar da dukkanin sojojinta daga kasarv ta Iraki.