21 Janairu 2020 - 14:54
Iran: Ministan Harkokin Wajen Oman Ya Isa Birnin Tehran

Ministan harkokin wajen kasar Oman Yusuf Bin Alawi ya isa birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, domin ganawa da jami’an gwamnatin kasar.

Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA-ta rawaito cewa: Bin Alawi ya isa birnin Tehran da safiyar yau Talata, inda ya samu tarbe daga takwaransa na Iran Muhammad Jawad Zarif, kuma suke ci gaba da ganawa.

Har yanzu babu wani bayani dangane da manufar ziyarar ta ministan harkokin wajen kasar Oman, amma dai ana sa ran jin ta bakin ministocin kasashen biyu bayan kamala ganawarsu.

Kafin lokacin dai majiyoyin ma’aikatar harkokin wajen Iran sun sanar da cewa bangarorin biyu za su tattauna kan wasu batutuwa da suka shafi halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakaiya, da ma wasu batutuwa na kasa da kasa.

Kasar Oman dai na daga cikin kasashen yankin tekun fash ad asuke da kyakkyawar alaka da kasar Iran, kamar yadda kasar ta sha taka rawa wajen ganin ta shiga tsakanin Iran da kasashen yammacin turai a takun sakar da ke tsakaninsu.