Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti
10 Disamba 2024
Labarai Cikin Hotuna Na Rakiyar Shahidan 11 Na Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Labanon A Garin "Shakra"
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: an raka tare da binne gawawwakin shahidai mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon 11 da suka yi shahada a garin Shaqra da ke kudancin wannan kasa tare da halartar dinbin mutane daban-daban.
10 Disamba 2024
Netanyahu: Faduwar Assad Wata Muhimmiyar Dama Ce Ga Isra'ila/ Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Da Aka Yi Da Syria A Shekarar 1974 Ba Ya Da Inganci
Gwamnatin Sahayoniya ta mamaye Al-Harmon (Jabal al-Sheikh) a kasar Siriya. A cewar wadannan kafafen yada labarai, gwamnatin yahudawan sahyoniya na shirin ci gaba da kai hare-hare kan kasar Siriya a cikin kwanaki masu zuwa.
10 Disamba 2024
Bayanin Shugaban Majalisar Malamai Na Mazhabar Ahlul-Baiti Ta Kasar Siriya Bayan Kifar Da Gwamnatin Bashar Assad/
Rayuka Da Dukiyoyi Da Wurare Masu Tsarki Na 'Yan Shi'ar Siriya Na Cikin Aminci.
10 Disamba 2024
Labarai Cikin Hotuna Na Bikin Karrama Malaman Kur'ani A Jihar "Katsina" Ta Najeriya
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: an gudanar da bikin karrama malaman kur’ani a karkashin jagorancin Sheikh Yaqub Yahya a garin Batagaro na jihar Katsina a Najeriya.
10 Disamba 2024
Sahayoniya Na Ci Gaba Kutsawa A Kasar Siriya Kilomita 20 Kawai Tsakaninsu Da Babban Birnin Siriya
Kilomita 20 Kawai Ke Tsakanin Tankokin Isra'ila Da Damascus/ Isra'ila a wani sabon salon tana kashe manyan masana da manyan malaman kasar ta Siriya
9 Disamba 2024
Isra'ila Na Shirin Kai Wani Mummunan Hari Kan Ƙasar Yemen
Tashar "Kan 11" ta gwamnatin Sahayoniya ta ruwaito cewa: Sojojin Isra'ila na shirin wani gagarumin hari da zasu kai kan kasar Yemen" martani bisa ga harba makamai masu linzami 2 zuwa Isra'ila a cikin kwanaki 2 da suka gabata da Yemen ta yi.
9 Disamba 2024
Bidiyoyin Yadda Isra'ila Ta Mamaye Garuruwa Biyu A Cikin Kasar Siriya
Amurka na sane da matakin da gwamnatin Sahayoniya ta dauka na mamaye wani yanki na kasar Siriya
8 Disamba 2024
Kai Tsaye Isra'ila Ta Tuntuba 'Yan Ta'addan Hay'at Tahrir Sham A Siriya
Bidiyon Yadda Mutane Suka Shiga Gidan Bashar Assad Da Wawashe Kayan Da Ke Ciki
8 Disamba 2024
Mamayar Gwamnatin Sahayoniya Ga Kudancin Siriya; Tankunan Yaƙin Isra'ila Sun Tsallaka Shingen Kan Iyakar Siriya
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun shiga yankin "Al Quneitra" da ke kudancin kasar Siriya tare da tankokin yaki.
8 Disamba 2024
'Yan Ta'addan Siriya Sun Sanar Da Hambarar Da Gwamnatin Siriya A Hukumance + Bidiyo
Gidan talabijin na kasar Syria da ke karkashin ikon 'yan adawa dauke masu ɗauke da makamai ya sanar da hambarar da gwamnatin Bashar Assad da gwamnatin Baath a Syria.
5 Disamba 2024
'Yan Ta'addar Takfiriyya Sun Shiga Birnin "Hama" Na Kasar Siriya
'Yan Ta'addar kungiyar takfiriyya ta "Tahrir Sham" sun shiga cikin birnin "Hama".
5 Disamba 2024
Manyan Munasabobin Da Suka Faru A Ranar 3 Da 5 Ga Watan Jumadas Sani
Wannan Rana Tana Daya Daga Ranekun Da Aka Ruyawaito Shahadar Sayyidah Fatimah As Kasancewar Matsalar Rubutu Da Aka Samu Wajen Rubuta Ranar Da Tayi Shahada Daga Ciki Akwai Wannan Rana Kamar Yadda Ruwayar Kwanaki 95 Ta Nuna.
5 Disamba 2024
Sanin Yanayin Rayuwar Zamantakewar Sayyidah Fatimah (AS) A Makka Da Madina
Boyuwar kabarin Sayyidah Fatimah (AS) a tarihi yana nufin ci gaba da yunkurinta da kuma alamar kin yardarta da ya faru a tarihi ne, kuma wannan kin amincewa za ta kare ne a lokacin da rayuwar tsarin sarauta da na kama karya yazo karshe a duniyar Musulunci, sannan kuma tsarin Imamanci na Muhammadiyya ya samu farfadowa tun daga farko da kuma samuwar tabbatarsa
5 Disamba 2024
Tunawa Da Shahadar Sayyidah Fatimatuz Zahra’a As 03/Jumadal Akhir/ 11/ Bayan Hijra
Sayyida Zahra (A.S) tabi Matakai guda biyar zuwa shida da Sayyidah Zahra'a A's ta bi wajen kare Imamin Zamaninta Da Wilayarsa ga su kamar haka: 1- Matakin farko na kasancewarta a bayan kofa. 2- Mataki na biyu shi ne halartar masallaci da gabatar da hudubar Fadak da rokon jama'a da su taimaka wa Imamin Zamanin Su Wato Imam Ali(a.s). 3- Mataki na uku shi ne take gidajen Ansar har darare 40 tana mai nemi taimako daya bayan dayansu domin su taimakawa Ali As Amma ba su amsa ba...
3 Disamba 2024
Falasdinawa 36 Sukai Shahada A Hare-Haren A Yau A Zirin Gaza
Majiyoyin ma'aikatar lafiya sun sanar da cewa ya zuwa yanzu Falasdinawa 36 ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin gwamnatin yahudawan sahyoniya suka kai a zirin Gaza a yau.
3 Disamba 2024
Isra'ila Na Ci Gaba Da Karya Yarjejeniyar Tsagaita Buɗe Wuta Da Labnon / 'Yan Ƙasar Lebanon 6 Sun Yi Shahada A Harin
Tawagar sa ido kan tsagaita bude wuta ta isa Lebanon
1 Disamba 2024
Dakarun Syria Na Ci Gaba Da Kwato Yankunan Arewacin Hama Da Kudancin Idlib Daga Hannaun ‘Yan Ta’adda + Bidiyo
Bayan ci gaban da 'yan ta'addar Tahrir al-Sham suka yi cikin sauri, bisa matakan da kwamandojin Siriya suka dauka da kuma fagen gwagwarmaya, an daidaita layukan tsaron gaba a arewacin birnin Hama tare da 'yantar da garuruwan da suka shiga hannun ‘yan Ta’adda.
1 Disamba 2024
Isra’ila Ta Kara Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Karo Na 62 A Lebanon; Bayyanar Jiragen Sama Marasa Matuka A Beirut
Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah har sau 24 a ranar Asabar din da ta gabata, kuma ta haka ne adadin karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta ya kai sau 62 tun bayan farawarta a ranar Laraba
1 Disamba 2024
Biranen 'Yan Shi'a Na Nubl Da Al-Zahra A Arewacin Siriya Sun Fada Hannnun ‘Yan Ta’adda
Garuruwan Nubl da Al-Zahra sun kasance mazaunin kusan mutane 60,000 na 'yan Shi'a Isna Ashariyya na kasar Siriya, kuma a ko da yaushe wadannan garuruwa biyu na Shi'a suna fuskantar hare-hare daga kungiyoyin takfiriyya tun farkon rikicin kasar Siriya.
1 Disamba 2024
Kofar Rago Ga Kungiyoyin Takfiriyya A Kofar Birnin "Hamah" A Kasar Siriya / 'Yan Ta'adda Sun Shiga Lardunan "Halab" Da "Idlib"
Idan dai ba a manta ba a safiyar ranar Laraba 27 ga watan November 2024 ne 'yan ta'addar takfiriyya karkashin jagorancin kungiyar Tahrir al-Sham (tsohuwar kungiyar Al-Nusra) suka fara wani gagarumin farmaki daga yammacin birnin Halab. sun sami damar kame wani babban yanki na birnin Halab da yankunan da suka mamaye. A mataki na gaba, wadannan 'yan ta'adda na neman ci gaba zuwa wasu manyan biranen kasar Siriya.