Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

24 Afirilu 2024

19:02:20
1453789

Yakin Uhudu Da Shahadar Sayyaduna Hamza As

A irin wannan rana ta 15 ga watan Shawwal ne a shekara ta uku bayan hijira ne dai yakin Uhud ya Auku tsakanin Mu’uminai bisa jagorancin Annabi Muhammad Sawa da Mushrikan Larabawan Makka akusa da dutsen Uhud da zimmar daukar fansar Yakin Badar da ya wakana kusan shekara daya data gabata.

                     Bayan mushrikai sun sha kayi a yakin Badar sun fara shirin daukar fansa ta hanyar yin shirin yaki bisa shugabancin Abu Sufyan. Wanda ya kasance Annabi da sauran Muhajirai sun so ayi yakin a cikin Madina ne, amma wasu Sahabbai wanda suka hada da Sayyidana Hamza As sun so ayi a wajen madina ne wanda daga karshe Annabi Sawa yayi azama suka fita daga cikin birnin Madina yakin ya kaure wanda a  farkon yakin Mu’uminai sunyi nasara akan Mushrikai har sun korasu.           Amma daga bisani sai wasu gungu na Sahabbai masu kibau bisa jagorancin Abdullahi dan Jubair da Annabi ya sanya su tsaron bayan Rundunar Mu’uminai suka gangaro don gani cewa mu’uminai sunyi nasara duk da Annabi Sawa yace masu karsu motsa daga gurin da suke komai zai faru, inda saukowar su ya sanya Mushirikai bisa Jagorancin Khalid Bin Walid suka yiwa Rundunar Mu’uminai qawa suka zagaye su ta baya inda hakan yasa mu’uminai suka tarwatse tare da guduwa.    Babu wanda yayi saura tare da Annabi Sawa sai dai yan mutane kadan na farkon su shine Imam Ali As inda yayi ta kore Rundunar Mushrikar daga wajen Manzon Allah Sawa wanda a wannan yakin An jima Annabin rahama ciwo a goshi tare da karyewar hakuransa guda biyu nagaba.

            Kuma a wannan yakin ne Sayyiduna Hamza Yayi Shahada inda bawan Hindu bisa umarninta ya soke shi da mashi. Inda adadin wadanda sukai shahada daga mumunai yakai 70 kuma manzon Allah Sawa yayi salla ga kowane daya daga cikin su shi kadai kuma a kowace sallah yana sanya gawar Sayyiduna Hamza As a kusa da kowani gawa da zai wa sallah kunga kenan shi Sayyiduna Hamza As Annabi Sawa ya masa salla sau 70 da wani abu kenan wanda gaba dayan su anbinne su ne akusa da wannan Dutsen na Uhud kamar yadda sunayen su yazo a Littafan tarihi. Suma mushirikai an kashe masu adadin daya kai sama da 20

            Bayan yakin Uhud Sayyidah Fatimah As ta samu labarin abun yafaru a yakin da kuma jiwa manzon Allah ciwo da akayi saita yunkura ta tafi fagen yakin tare da wasu gungu na mata inda suka dauki ruwa da kayan abinci suka tafi da shi inda suka bawa wadanda da suka ji ciwo ruwa suka sha tare da daure guraren da suka ji ciwon inda Sayyidah Fatimah As da kanta ta kula da mahaifinta tare da wanke masa fuskarsa inda ta kona guttun tabarma ta sanya tokar a jikin ciwon don jinin ya dena zuwa.

 Kamar yadda Alkur’ani yayi nuni da faruwar wannan yakin acikin surar Al’Imran daga ayata 121 zuwa ta 171.