Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

21 Afirilu 2024

12:04:55
1452932

Alkur'ani Mai Girma Ya Tsara Yadda Al'ummar Musulmi Zasu Sa Ke Gina Makomarsu Da Kuma Karfafa Karfinta Don Samun Nasara

﴾Manzon Allah Muhammad {s.a.w}, da wadanda ke tare da shi sun kasance masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu zaka gan su suna masu yin ruki’I da sujada, suna neman wata falala daga Allah da yarjewarsa, alamarsu tana ajikin fuskõkinsu na daga alamun sujjada﴿. Akwai bukatar al'ummar musulmi su karanta suratul Fath a tsanake domin tsara makomarta, da gina karfinta, da kuma dawo da martabarta a duniya.


Mafi kyawun sifa da Alkur’ani ya siffanta ga muminai ta zo ne a aya ta 29 a cikin Suratul Fath:

﴿مُّحَمَّدٌ رَّسُولُ اللَّهِ وَالَّذِينَ مَعَهُ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ تَرَاهُمْ رُكَّعًا سُجَّدًا يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِّنَ اللَّهِ وَرِضْوَانًا سِيمَاهُمْ فِي وُجُوهِهِم مِّنْ أَثَرِ السُّجُودِ﴾.

﴾Manzon Allah Muhammad {s.a.w}, da wadanda ke tare da shi sun kasance masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu zaka gan su suna masu yin ruki’I da sujada, suna neman wata falala daga Allah da yarjewarsa, alamarsu tana ajikin fuskõkinsu na daga alamun sujjada﴿. Akwai bukatar al'ummar musulmi su karanta suratul Fath a tsanake domin tsara makomarta, da gina karfinta, da kuma dawo da martabarta a duniya.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA –  ya kawo maku bayani dangane da makomar al’ummar musulmi a mahangar alkura’ni inda ya fara da cewa: al'ummar musulmi na bukatar karanta suratul Fath domin tsara yadda za su gina makomarsu, da karfafa karfinsu, da kuma dawo da matsayinsu a duniya, kamar yadda siffar al'ummar akan kanta ke na daya daga cikin muhimman hanyoyin samun karfinta.

Akwai bukatar al'ummar musulmi su karanta suratul Fath a tsanake domin tsara yadda za su gina makomarsu, da gina karfinsu, da kuma dawo da martabarsu a duniya, domin siffar al’umma tana daya daga cikin mabubbugar karfinta, kuma duk lokacin da wannan siffa ta bayyana karara to muminai zsau samu damar samun janyo zukata da hankula. Babu abun yafi kyau na siffa sama da wacce ALkur’ani mai girma ya siffanta su da ita  a cikin aya ta 29 surar Fath, da ke cewa:

﴿مُّحَمَّدٌ رَّسُولُ اللَّهِ وَالَّذِينَ مَعَهُ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ  تَرَاهُمْ رُكَّعًا سُجَّدًا يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِّنَ اللَّهِ وَرِضْوَانًا سِيمَاهُمْ فِي وُجُوهِهِم مِّنْ أَثَرِ السُّجُودِ﴾.

Allah Ta’ala ya girmama Manzonsa ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa ) da wadanda suke tare da shi da wannan siffa mai haske da ke bayyana sifofinsu, da cewa suna fara rayuwarsu daga akidarsu ne, kamar yadda ita kayyade halayensu da manufofinsu. Suna mu'amala da kafirai da tsanani da karfi da jarumtaka suna fushi da fushin Allah, kuma a shirye suke su tunkari bata da sadaukarwa domin addininsu da imaninsu.

Wannan yana bayyana mana yadda musulmi duk da raunin kayan aikinsu da karancinsu, sun sami nasarori masu girma da kuma kwato al'umma daga bautar azzalumai.

Sai dai kuma karfin muminai da jajircewarsu wajen tunkarar rundunar kafirci bai isa ya bayyana irin gagarumar nasarar da suka samu ba. Akwai daya siffar tasu wacce ta budewa musulmai zukatan al’umma har ta kai su ga karkata zuwa ga sakon Musulunci, wannan sifa ita ce rahama, wadda ita ce ginshikin wayewar dabi'un da musulmi suka sami mallakar kwazo na zukatan mutane da ita.

Mutane sun ga yadda rahama ke siffanta tantance halaye da dabi’un muminai, kuma wannan rahamar ta hada da tsarin kyawawan dabi'u, wadanda suka hada da kyautatawa, fifita wasu akansu, karimci, kyauta, adalci, son alheri, da neman uzuri yayin da wani ya zame ya yi kuskure. Muminan da suka kebanta da siffantuwa da rahama sun cancanci kafa adalci a bayan kasa.

Idan yaki ya kare to sai halin rahama ya bayyana, don haka mumini sai ya yi mu'amala da hakurinsa da kyawawan dabi'unsa ga 'yan uwansa, da kuma duk musulmin da ya ga dama da son ransa ya shiga Musulunci bayan ya ga bayyanar kyawawan dabi'un muminai... wanda shine abin da muke kira a wannan zamani da karfi na jan hankali, wanda ya hada da al'adu, koyarwa, dabi'u, da wayewa.

Da dukkan jajircewa da tsayin daka da jarumta, musulmi sun yi ta fama da kafirai a yakin ‘yantar da kai, tare da samun nasarorin a lokacin yakin da har yanzu suke rudar da masana tarihi, babu wani fage a cikin yaki sai nuna tsananin karfi, jarumtaka, jajircewa, karfin zuciya da azama. Don haka kafirai ba su da wani abin da ya wuce su ja da baya a gabansu saboda tsoron mayakan da za su yi guguwar kundunbala a cikin fili suna daga tutar gaskiya suna cewa: “Jihadi ne! na nasara ko shahada”.

Imani ne ya cika zukatansu da kwarjini, kuma suka kaddamar da tunaninsu don samar da ra'ayoyi da dama wadanda kafirai ba su yi zato ba, da kuma kirkiro salo da dabarun yaki, kuma ba wai kawai sun iya karfin yaki da takkub aba ne a’a sai dai karfin nasu ya bayyana cikin jajircewar zukata, da karfin tunani, da hasken azama, da azamar cimma nasara.

A yau za ku ga wani misali mai rai kuma misali na hakika da ke zaburarwa mutane kwarin guiwar wanda shi ne jajircewar Mujahidai muminai a Gaza, yayin da suke kalubalantar wannan mugunyar sojojin mamayar Isra'ila da makamansu masu sauki inda suka cika zukatansu da karfin gwiwa suna tunanin siffar Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) da wadanda suke tare da shi. Wannan sifar ya kasance mafi mahimmancin tushen ƙarfinsu suna fuskantar abokan gaba da ƙarfin da ya dace da su, kuma hakan ya zama wajibi a fagen fama.

Haka nan kuma suna raba dabino da busasshiyar biredi a tsakaninsu, kuma kowannensu yana fifita dan uwansa a kan kansa, kuma dabi'arsu ta zama nasara a gare su, domin yana janyo hankalin al'umma da kaunarsu ga dukkan ‘yantattu masu burin samun adalci, domin babu adalci sai da rahama, kamar yadda babu Nasara idan ba wahala ba... Kuma tsanani ga kafirai a fagen fama yana da alaka da rahama a tsakanin muminai, don haka goshinsu ya haskaka fuskokinsu na daga tasirin sujjada, ta yadda haske ke tafiya daga goshin masu sujjada zuwa zukatan dukkan ‘yantattun mutane a wannan duniya, inda zalunci ya fara fuskantar barazanar rugujewar ginshikansa, da girgizar harsashinsa, da rugujewar tsarinsa.

Tare da jajircewa da jarumta da jin kai, za mu iya sake gina wayewar Musulunci da dan Adam ke bukata a halin yanzu, wanda shi ya sa 'yantattun mutane ke kallon masu imani a zirin Gaza cikin kauna da ban sha'awa.