Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

20 Afirilu 2024

04:26:35
1452562

Battaliyar Sayyidush -Shuhada: Za mu mayar da martani ga koma waye ya aikata hakan

Yadda Isra’ila Ta Kai Harin Bama-Bamai A Sansanin Sojin Kalso Da Ke Lardin Babil Na Kasar Iraki + Bidiyo

Sansanin Kalso shine hedikwatar rundunar Hashdush-Shaabi ta kasar Iraqi, kuma wuri ne da sojoji masu sulke da sojojin bataliya ta 27 na kungiyar Hashdush-Shaabi suke.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA –  ya bayar da rahoton cewa: an samu tashin bama-bamai masu yawa a sansanin soji da aka fi sani da "Kalso" a kudancin birnin Bagadaza, wanda cibiyar hadin gwiwa ce ta sojoji da 'yan sandan tarayya da kuma dakarun Hashdush-Shaabi. Da farko dai an yi tunanin cewa wannan harin na Amurka ne, amma a hukumance ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta sanar da cewa ba ta da wani hannu a wannan harin, kuma jami'an Amurka - mai yiwuwa suna tsoron maida martini ne – shine suka bintawa  kafafen yada labarai cewa an kai wannan harin da mayakan gwamantin sahyoniyawa. A halin da ake ciki, Amurka bayan sanarwar cewa ba ta da hannu a harin, amma tana ci gaba da sanya ido kan rahotannin da aka samu game da shi.

Kamar yadda Kamfanin dillancin labaran Al-Mayadeen na kasar Lebanon ya fada cewa, mutum daya ne ya yi shahada, yayin da wasu 8 suka jikkata sakamakon fashewar wadannan abubuwa da a sansanin Kalso.

Battaliyar Sayyidush -Shuhada: Za mu mayar da martani ga koma waye ya aikata hakan

"Abuala Al-Walai" babban sakataren bataliyoyin Sayyidush -Shuhada na kasar Iraki yayin da yake mayar da martani kan abin da ya faru a sansanin soja na "Kalso" na "Al-Hashd al-Sha'abi" ya ce: Duk wanda ya kasance yana da hannun a wannan harin da aka kai kan sansanin Hashdush -Sha'abi, ko wane ne shi za mu mayar da martani.

Daraktan ofishin al-Mayadeen a birnin Bagadaza ya bayar da rahoton cewa, wadannan munanan hare-haren sun auna babbar kofar shiga sansanin na Kalso, da garejin mota da kuma ofisoshi biyu na dakarun Hashdsuh-Shaabi, kuma tsananin hare-haren na da karfi sosai.

Har ila yau rundunar Hashd al-Shaabi ta kasar Iraki ta tabbatar da wannan fashewar ta hanyar fitar da sanarwa tare da sanar da cewa, an samu fashewar wani abu a hedikwatar dakarun Basij da ke sansanin sojin Kalso da ke arewacin lardin Babil a kudancin Bagadaza.

A cikin sanarwar da rundunar 'yan sandan Iraki ta fitar, an bayyana cewa, tawagar bincike ta isa wurin da fashewar ta afku kuma wannan fashewar ta yi sanadiyar hasarar dukiya da jikkata wasu mutane.

Shugaban kwamitin tsaro na lardin Babil na kasar Iraki ya bayyana cewa, an samu wasu fashe-fashe 5 a sakamakon harin da jiragen yaki marasa matuka suka kai kan sansanin Basij Hashd al-Shaabi.

Har ila yau, wannan jami'in na Irakin ya kara da cewa, yawan wutar da ta tashi ta faru ne sakamakon yadda bishiyoyi ke kewaye da sansanin.