Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

25 Afirilu 2024

18:00:34
1454110

"Falasdinu; Ita Ce Babban Al’amarin Musulmi”.

Dangantakar Shi'a Da Batu Falasdinu Da Birnin Quds / Marajio'in Shi'a Su Ne Magoya Bayan Falasdinu

A matsayinmu na 'yan Shi'a, mun yi imani da cewa duk wani yanki na Musulunci ana daukarsa a matsayin wani bangare na al'ummar musulmi, kuma idan an kai hari ko aka mamaye shi, ya zama wajibi mu shiga filin domin 'yantar da shi.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa, batun Palastinu a ko da yaushe ya kasance abin da malamai da maraja'an Shi'a suka fi mayar da hankali a kai tun farkon mamayar, lamarin da ke nuna hankalin 'yan Shi'a ga kasashen musulmi ba tare da la'akari da kabila da mazahabar addini ba, kuma hakan yana nuna muhimmancin lamarin Palastinu a cikin tsarin tunani da nazarin mazhabar Ahlul Baiti (a.s), da kuma sani da tantance makiya da malaman Shi'a da Maraji'ai suke da shi.

A cikin wani bayani da “Rasoul Husain” ya rubuta ya yi magana kan alakar ‘yan Shi’a da Palastinu da kuma harami mai tsarki na Qudus ya kuma yi imani da cewa: lamarin Palastinu ya kasance abin da ya shafi ‘yan Shi’a tsawon shekaru da dama, musamman ma malaman taqlidi da na Shi’a. Wannan kula da al'amarin Palastinu a tsakanin malamai da maraja'an shi'a ya kasance tun kafin Imam Khumaini (RA) ne, kuma a yau Iran ta shiga fagen tallafa wa Falasdinu ta kowace fuska ba tare da la'akari da wata mazhaba da addini ba.

Sabanin tunanin da wasu ke yi a tsawon tarihi, malamai da marajian Shi'a sun bayyana cewa, lamarin Palastinu lamari ne mai muhimmanci da tushe na asali ga al'ummar musulmi, da cewa tun da farko makiya sun yi nasarar rage muhimmancin wannan lamari ta hanyar yada rarrabuwar kawuna da munafunci har ya zama wani abu maras muhimmanci a kasashen Larabawa. Bayan haka makiya sun fara raba kan Palastinu sannan kuma a hankali mamayar sahyoniyawan ta kara fadada.

Ta hanyar juyar da gaskiya tare da buga gangunan banbance-banbance na addini, kafafen yada labarai na ‘yan amshin shatan suna kokarin bullo da wani sabon makiyi ga al’ummar kasashen Larabawa maimakon gwamnatin sahyoniyawa, ta hanyar haifar da sabani na bangaranci da na addini ya zamo al’ummar musulmi sun karkata daga hanyarsu miƙakkiya. A cikin bayanin nasa, Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa makiya a cikin yakin ruwan sanyi suna neman ƙarfafa da girmama banbance-banbancen addini da kuma kokarin ganin an ajiye batun kiyayyar da akewa gwamnatin sahyoniyawa a gefe, wacce ake daukarta a matsayin makiyi ta farko.

Domin yin bayanin irin rawar da Shi'a ke takawa a lamarin Palastinu, ya kamata mu ambaci tafiyar daya daga cikin Maraji'an Shi'a zuwa Palastinu. Ayatullah Muhammad Husain Kashiful Ghiɗa'a Shi ɗaya ne daga cikin Maraji'an shi'a ya yi tafiya zuwa kasar Falasdinu a shekara ta 1931 inda ya halarci wani taron addinin musulunci da aka shirya domin tallafawa Palastinu tare da gabatar da jawabi mai matukar ban sha'awa a wannan taron wanda martanoni da dama sun biyo bayan bayanin nasa da ke nuna goyon bayan Falasdinu.

Batun Palastinu ya kasance mai karfi a cikin bayanan Maraji'an Shi'a, irin su Ayatullah Sayyid Muhsen Hakim da Ayatullah Khui da Ayatullah Muhammad Baqir Sadr da kuma Ayatullah Khamenei, kuma bayanan wadannan Marajio'in dangane da Falasdinu an tattara su a cikin littafi mai suna:

 (فلسطین؛ قضیة المسلمین الکبری)

"Falasdinu; Ita Ce Babban Al’amarin Musulmi”.

A matsayinmu na ‘yan Shi’a, mun yi imani da cewa duk wani yanki na Musulunci ana daukarsa a matsayin wani bangare na al’ummar musulmi, kuma idan aka kai masa hari ko aka mamaye shi, ya zama wajibi mu shiga filin daga domin ‘yantar da shi.