Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

23 Afirilu 2024

04:48:11
1453359

Spain: Idan Babu Kasar Falasdinu, Ba Za A Sami Zaman Lafiya A Yammacin Asiya Ba

Ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya jaddada matsayin gwamnatin kasar ta Spain na amincewa da kasar Falasdinu da kuma shigar da ita cikin Majalisar Dinkin Duniya.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA ya habarta maku cewa: "Mayar da sulhu tsakanin kasashen biyu, yana nufin samar da tabbataccen zaman lafiya da ba za a iya dawo da shi ba," in ji Albares a wannan Litinin ga manema labarai a lokacin da ya isa Majalisar Harkokin Waje ta Tarayyar Turai (EU) a Luxembourg.

Albares ya nanata cewa Madrid na ci gaba da neman hakan "yanzu fiye da kowane lokaci" da a tsagaita bude wuta na dindindin a tunkarar harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke shirin kaiwa Rafah, a kudancin zirin Gaza.

Ya kuma bukaci a bude dukkan wuraren kan iyaka domin taimakon jin kai ya samu shiga yankin da ke gabar teku.

A cikin 'yan watannin nan hukumomin Spain sun sha sukar hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza tare da jaddada bukatar daukacin duniya su amince da kasar Falasdinu. Kasar Spain ta goyi bayan hukuncin da kotun duniya ta yanke kan kisan kiyashin da Isra'ila ta ke yi a Gaza.