Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

20 Afirilu 2024

04:51:46
1452565

Salon Yanayin Rayuwar Ahlul Baiti (AS);

Muhimmancin Addu’ah A Wasiyyar Amirul Muminin (AS) Ga Imam Hassan Mujtabi (AS) + Bidiyo

Jagoran juyin juya halin Musulunci: A duk lokacin da kuka fara magana da Allah da kuma bayyana bukatarku, Allah Madaukakin Sarki zai ji muryarku da bukatarku. A koda yaushe kuna iya magana da Allah, kuna iya yin zance da shi, za kuna iya tambayarsa. Wannan babbar dama ce da albarka ga dan Adam.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA –  ya kawo maku bayanin jagaoran juyin juya halin musulunci dangane muhimmancin addu’a ind aya fara da cewa: mafi girman sifofin addu’a shi ne alaka da Allah da kuma jin cewa kai bawane, kuma an gabatar da ita a madogaran addini a matsayin wata hanya ta samar da tawali’u da tawakkali kuma nisantar ganin kai wani ne da son kai.

Idan kuma mutum, baya ga samun alaƙar zuciya da Allah, kuma ya mai da hankali ga manyan koyarwar addu’o’i masu inganci, zai fahimci tekun tsarkakakkiyar koyarwar Ubangiji kuma ya sami hakikanin ibada.

Dangane da haka ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayin hudubar sallar Juma'a ta shekara ta 1385 ya yi bayani kan muhimmancin Addu’ah a cikin maganganun Ahlul Baiti (a.s) inda ya ce: A cikin wasiyyar Amirul-Mu’minin (a.s.) ga Imam Hasan Mujtaba (a.s.), wannan ma’anar maganar tana kunshe acikinta da cewa: “اعلم انّ الّذی بیده خزائن ملکوت الدّنیا والاخرة قد اذن لدعائک و تکفّل لاجابتک” “ka sani Allah wanda a hannunsa taskokin duniya da lahira su key a baka damar ka roke shi kuma ya dauki nauyin amsa maka" ma’ana Allah maɗaukakin sarki wanda yake da ikon sama da ƙasa duka a cikin ikonsa, ya ba ka damar yin addu'a da magana da shi, ka tambaye shi ka roke shi. " وامرک أن تسأله لیعطیک" ya umarceka da ka roke shi ya ba ka. Wannan alakar roko da karba daga wurin Allah ita ce dalilin daukakar ruhin dan Adam kuma ita ce ke karfafa ruhin ibada. " و هو رحیم کریم لم یجعل بینک و بینه من یحجبک عنه" Allah Madaukakin Sarki bai sanya dan tsaka-tsaki ko tazara ko wani shamaki tsakaninsa da kai ba. Duk lokacin da kuka fara magana da Allah da bayyana bukatunku, Allah Madaukakin Sarki zai ji muryarku da rokonku. Kullum ako da yaushe kuna iya magana da Allah, kuna iya yin zance da shi, za ku iya tambayarsa da rokonsa. Wannan babbar dama ce da ni’ima ga dan Adam.