Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

21 Afirilu 2024

10:31:44
1452913

Jami'an Amurka: Ƙarfin Sojanmu A Yankin Bai Isa Ya Fuskanci Iran Ba

Jami'an Amurka suna ganin cewa karfin sojan da wannan kasa ke da shi a yankin gabas ta tsakiya bai isa ya tunkari kasar Iran ba idan har aka yi yaki kai tsaye tsakanin Iran da gwamnatin sahyoniyawa.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Kafar yada labaran yahudawan sahyuniya ta bayar da rahoton cewa, biyo bayan martanin da Iran ta mayar, martanin da ba a taba ganin irinsa ba dangane da munanan ayyuka na gwamnatin sahyoniyawan a lokacin da ake gudanar da harin Iran da akewa taken "Tabbataccen Alkawari" da kuma tashe-tashen hankula a yankin, jami'an Amurka sun yi imanin cewa karfin sojan wannan kasa a yankin na fuskantar Iran a lamarin yakin kai tsaye tsakanin Iran da gwamnatin sahyoniyawa bai wadatar ba.

Bayan da Iran ta mayar da martani kan harin da gwamnatin sahyoniyawa ta kai kan ginin karamin ofishin jakadancinta da ke Damascus a harinta mai taken aikin "Tabbataccen Alkawari" " tare da goyon bayan da sojojin Amurka suke yi wa manyan kawayenta a yankin, kafar yada labaran yahudawan sahyuniya ta bayar da rahoton cewa, jami'an Amurka na yanzu da na tsoffin jami'an Amurka sun yi imani da cewa;  sojojin Amurka ba a shirye suke ba wajen tunkarar wani dogon rikici da ka iya barkewa a yankin ba, kuma mai yiwuwa ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta sake yin la'akari da bukatun sojin idan wannan rikici ya kara tsananta a yankin.

Da yammacin ranar Asabar din da ta gabata ne Iran ta kaddamar da farmakin "Tabbataccen Alkawari" kan wasu yankunan da aka mamaye a matsayin martani ga mummunan matakin da aka dauka kan cibiyoyin diflomasiyyarta, wanda ya yi sanadin shahadar kwamandojin soji 13 da ma'aikatan ofishin jakadancinta a Damascus.

A yayin wannan farmakin da Iran ta bayyana a matsayin wani takaitaccen aiki da nufin ladabtarwa ga muggan ayyukan gwamnatin sahyoniyawan, an harba jiragen yaki marasa matuka da makamai masu linzami kan yankunan da aka mamaye.

Kafofin yada labarai na Ibraniyawa sun ba da labarin wannan harin: Harin da Iran ta kai a ranar 14 ga Afrilu shi ne hari mafi inganci wanda aka gudanar da shi a bayyane da sanin kowa tare da ingantattun makamai masu linzami a tarihin tsaron duniya. An harba jiragen ne daga sansanoni da dama da kuma tazara tsakanin kilomita 1000 zuwa 1500.

Jaridar The Times of Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, duk da cewa Iran ta jaddada cewa ba ta neman fadada zaman dar-dar a yankin ne ta hanyar shiga yakin basasa, kuma manufarta kawai ita ce ta hukunta gwamnatin sahyoniyawan da ta'addancin da take yi. "Michael Mulroy", daya daga cikin tsoffin mataimakan sakataren tsaron Amurka mai kula da harkokin yankin yammacin Asiya a gwamnatin Donald Trump ya ce, "Ba na jin za mu sami isassun sojojin da za mu tallafa wa Isra'ila (a yankin) a cikin lamarin yakin kai tsaye tsakanin su da Iran”.

Tun bayan harin "Guguwar Aqsa" da aka yi a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda kungiyar Hamas ta kaddamar da hari ga gwamnatin sahyoniyawan da kuma fara yakin Gaza, wanda ya haifar da karuwar tashe-tashen hankula a yankin yammacin Asiya, Amurka ta aike da dubunnan sojojinta zuwa yankin, wanda A cikin shekarun da suka gabata, adadinsu ya ragu a hankali.

Amurka wacce ta haifar da rashin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ta hanyar fara munanan yake-yake a kasashen Afganistan da Iraki, ta yi ikirarin cewa ta ci gaba da rike sansanonin soji a wadannan kasashe domin taimakawa dakarun cikin gida na Iraki da Siriya wajen yaki da kungiyar ISIS a yankin .

Sai dai da yawa daga cikin sojojin Amurkan da aka tura a baya-bayan nan zuwa yankin jiragen ruwa ne da jiragen yaki da ake turawa yankin na wani dan lokaci.

Wannan kafar yada labaran yahudawan sahyoniya ta yi ikirarin cewa rikicin da ake fama da shi a yankin na yanzu yana gwada dabarun Amurka ya dogaro da tura sojoji ne.

An bayyana a cikin wannan labarin cewa: "Joseph Votel", daya daga cikin manyan hafsoshin sojojin Amurka hudu masu ritaya, wanda ke kula da rundunar sojojin Amurka a yammacin Asiya, ya ce, "Ma'anar wannan halin da ake ciki ga sojojin Amurka shi ne ya mu sake tunani a kan irin muhimman abubuwan da muke bukata a yankin,."

Duk da ikirari da tsohon shugaban CENTCOM Votel da wasu tsoffin jami'an Amurka suka yi game da nasarar da Amurka ta samu na taimakawa Isra'ila wajen dakile manyan hare-haren jirage marasa matuka da makamai masu linzami da Iran ta kai ya ce, "Ina ganin babban abin da ke damun mu shi ne yadda za mu iya mayar da martani cikin gaggawa cikin dogon lokaci ne”.

Jami'an Amurka sun ce, da alama Iran ba ta neman cikakken yaki da gwamnatin yahudawan sahyoniya, don haka Tehran ta dauki lamarin Isfahan da martanin da ta ke yi na tsaron sararin samaniya kan kutsawar wasu kananan jirage a matsayin abu maras muhimmanci. Sai dai masana sun yi gargadin cewa halin da ake ciki ba shi da tabbas, musamman ganin yadda ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin gwamnatin sahyoniyawan da Hamas a zirin Gaza.

Bisa nakaltowa daga wannan shafin sadarwar, ministan harkokin wajen kasar Iran Husain Amirabdollahian, wanda ya je birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron komitin sulhu na MDD ya bayyana cewa, kasar Iran ba ta da wani shiri na mayar da martani, sai dai idan har gwamnatin sahyoniyawan ta yi wani babban matakin hari.

Babban jami'in diflomasiyyar na Iran ya ci gaba da cewa: Matukar dai ba a samu wani sabon wauta daga Isra'ila da ya saba wa muradunmu ba, to kuwa ba za mu yi wani sabon martani ba.

Sai dai ya yi gargadin cewa idan gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa Iran hari, za ta karo da wani martani mai tsanani kuma mai tsauri, sannan ya ci gaba da cewa: Idan Isra'ila ta dauki wani mataki mai tsanani kan kasata kuma hakan ya tabbata gare mu, to za mu mayar da martani nan take da zai sa suyi nadama.

A wani bangare na rahoton wannan kafar yada labaran yahudawan sahyoniya ta bayyana cewa: Jami'ai sun ce tura karin sojojin Amurka zuwa yankin yammacin Asiya da kuma karfafa cibiyoyin leken asiri na tsawon lokaci yana da alaka da matsalolin.

Wani jami’in kasar Amurka, bisa sharadin kada ya bayyana sunan sa, ya ce: Sojojin (Amurka) sun warwatsu a kasashen Turai, wadanda kuma ba su nan, suna hutu kuma suna samun hutu Duk da haka, ya kamata a mai da hankali kan Asiya.

Mulroy ya ce, kamata ya yi Amurka ta karfafa matsayinta a yankin, ba tare da yin watsi da mayar da hankali kan kasar Sin ba, kana ta ba da fifiko kan barazanar da ke tattare da ita.