Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

20 Afirilu 2024

05:16:23
1452572

Yanayin Rayuwar Ahlul Baiti (AS)/ Alkur'ani Shi Ne Mafifici Kuma Makaranta Ta Farko

Yanayin Rayuwar Ahlul Baiti (AS)/ Alkur'ani Shi Ne Mafifici Kuma Makaranta Ta Farko

Shugabanni Imamai masu tsarki ma’asumai (a.s) da suka hada da Imam Riza (a.s) su ne masu yada Alkur’ani, kuma Alkur’ani shi ne mafifici kuma mazhabar farko da ta nuna asali ta hanyar magance munanan dabi’u da samun kyawawan halaye.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA –  ya kawo maku bayani dangane da littfai mai tsraki na Alkur’ani: an samo daga Tsarkakkun Imamai ma’asumai, ciki har da Imam Rida (AS) inda ya suka ce: Ba rin aikata munanan dabi’u ababen kyama yana daga kyawawan halaye.

Idan muka lura da rayuwar Imam Riza (a.s) za mu ga yanayin kyakkyawar rayuwa wacce ake so, wanda a cikinta ba a samu munanen halaye marasa dadi ba, sai dai kawaia kyawawan hayale ne masu ababen so. A fili yake cewa kula da rayuwar wannan Imami mai daraja na iya jawo tafarki madaidaici a gaban idanunmu; Da sharadin cewa mu duba da kyau mu kalli dabi'ar yanayin mu’amalar Imam din, ba wai a bayyane kawai ba, a’a tare da lura mai da kyau zamu gano da samun mabunbugar halayen Ubangiji na wannan Imami mai daraja.

Imam Riza, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne ma'abocin yada Al-Qur'ani da karantarwarsa, kuma Alkur'ani shi ne mafificin girma kuma makarantar farko wadda ta nuna asalin hanyar magance munanan dabi'u da samun kyawawan halaye.

A hangen mutum daya, Alkur'ani ba littafi ne na gama gari ba ko kuma wani babban littafi ne kawai ba, a’a a wurinsa Alkur'ani wata hakika ce da ta wuce tunani. Littafi ne da Allah ya bayyana kansa a cikinsa da dukkan kyawunsa kuma wanda ya samo asali ne daga cikakken iliminsa da cikakkiyar rahamarsa.

Babban abin da ke tattare da makadaicin Allah shi ne alakarsa da Allah, don haka daya daga cikin tsare-tsare masu muhimmanci a rayuwarsa shi ne jin muryar Ubangiji, wadda ta fi kowane magana da tsare-tsare, wacce take da matsayin kamar fifikon Allah a kan halittu.

An karbo daga Imam Sadik (As) cewa ya kasance yana cewa: “Idan na karanta Alkur’ani a cikin Sallah, ina ji kamar na ji ne daga Allah ne.

Imam Riza, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya na yin tunani a kan kowace aya ta Alkur’ani da ya karanta. Ya na ajiye Al-Qur'ani a cikin zuciyarsa ta yadda yawancin maganganunsa da amsoshinsa ya ciro su ne daga Alqur'ani.

Littafin Rayuwar Tauhidi- kadaita Allah- daga Mahangar Imam Rida (a.s.) Farfesa Sheikh Muhammad Hasan Wakili ne ya rubuta shi. Za mu yi bitar wani sashe na wannan littafi domin sanin salon rayuwar tauhidi na Imam Rida (a.s.).