Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

23 Afirilu 2024

11:05:34
1453447

Gwamnatin Sahayoniya Ta Na Sace Sassan Jikin Shahidan Palasdinawa

Kakakin ma'aikatar lafiya ta Gaza ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra'ila na sace sassan jikin shahidan Falasdinawa, sannan su kai gawarwakin zuwa zirin Gaza su bawa mazaunanta.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA - ya habarta maku cewa: Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce Isra'ila na sace sassan jikin Falasdinawa da suka yi shahada.

Dr. Ashraf al-Qadara ya ce: "Wannan ba shi ne karon farko da muka samu labarin cewa 'yan mamaya na Isra'ila suna yankawa da sace sassan jikin shahidan (Falasdinawa) ba." Suna kai wadannan gabobin zuwa wani wuri sannan su dawo da gawarwakin zuwa zirin Gaza su bada su ga mazauna wurin.

Kakakin ma'aikatar lafiya ta Gaza game da abin da Isra'ilawa suke yi da sassan jikin wadannan shahidai? Ya ce: 'Yan mamaya na Isra'ila suna yin kashe-kashe da kisan kiyashi a kowane yanki da wurin da suka shiga, sannan su kai wadannan gawarwaki zuwa wani yanki da ba a san ko ina ba a cikin Isra'ila suna sace gabban wadannan gawarwakin. Kuma suna gudanar da bincike da suka shafi gwajin DNA da makamantansu.

Ya kara da cewa: Za a iya amfani da gabobin da aka sace a hannun gwamnatin Palastinu a cikin binciken kimiyya da sauran ayyuka.