Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

25 Afirilu 2024

13:23:25
1454007

Ayatullah Ramezan Ya jaddada Hakan Ne A Ganawar Da Ya Yi Da Shugaban Ƙasar Venezuela;

Hankali Da Ruhiyya Da Adalci Su Ne Ɓangarori Uku Na Nazarin Shi'a

Ayatullah Reza Ramezani, Sakatare-Janar na Majalisar Duniya ta Ahlul-Bait (AS) ya gana tare da tattaunawa da Shugaba Nicolas Maduro a ziyarar da ya kai kasar Venezuela.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Reza Ramezani, Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya gana da shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro a ziyarar da ya kai kasar Venezuela.

A farkon wannan ganawar, shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro, yayin da yake bayyana farin cikinsa da ziyarar Ayatullah Ramadani a kasar ta Venezuela, ya dauki alakar Iran da Venezuela a matsayin tsohuwar alaƙar 'yan uwantaka, mai zurfi, inda ya bayyana cewa: ya kamata wadannan alakokin su dace da dabi'u da ka'idoji. Muna rayuwa a cikin duniya mai cike da zalunci, amma babu wanda ya ke da ikon Rayuwa cikin 'yanci cikin salama, da samun yancin ruhi da al'adu da addini.

Nicolas Maduro a yayin da yake ishara a ganawar da ya yi da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya dauke shi a matsayin mutum mai Basira da hangen nesa wanda yake da cikakken nazari da zurfin nazari kan duniya da abubuwan da suke faruwa inda ya ce: A ko da yaushe muna amfani da nusatarwar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran. kuma muna neman babban sakataren majalisar duniya na Ahlul-Baiti (a.s.) ya mika gaisuwata ta musamman ga Ayatullah Khamenei.


Sahayoniyawa Ne Ke Tafiyar Da Amurka


Ya ci gaba da cewa: Dukkan matsalolin da ake fuskanta a duniya a yau sun samo asali ne daga wannan ra'ayi na fasikanci da mummunan Rayuwa da ke da tasiri a dukkan ginshikan kasashen yammacin duniya. A yau, yahudawan sahyoniya suke mulkin Amurka kuma manyan kasashe biyu, karfin soji da cibiyoyin sadarwar jama'a, suna karkashinsu ne.

Shugaban kasar Venezuela ya kara da cewa: Tabbas, a yau mun shiga duniya mai ɗauke da ikon sassan duniyoyi daban-daban inda aka kafa tantina daban-daban na madafun iko irin su China, Rasha da Iran.


Dangantaka Mai Zurfi A Cikin Dabarun Aiki Tsakanin Iran Da Venezuela


A cigaba da wannan taro, Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya dauki alakar Iran da Venezuela a matsayin alaƙa mai zurfi da nagarta in da ya fayyace cewa: yin zalunci da yarda da zaluncin abun Allah wadai da ne bisa tsarin addininmu, kuma a daya bangaren, an jaddada umarni da karamci da adalci.

Ya ci gaba da cewa: Tsayin daka a gaban zalunci wani babban darasi ne da Imam Khumaini (RA) ya koyar da mu kan tafarkin wayewa. Imam Khumaini (RA) ya yi imani da rukunan Imani guda hudu, wadanda suka hada da imani da Allah, da imani da manufa, da imani da tafarki da imani da mutane. A bisa wadannan akidu da rukunnan imani guda hudu Imam ya yi juyin juya hali tare da kawo cikas ga yanayin da ke gudanar da duniya.

Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya kara da cewa: Dole ne a samu sauye-sauye a duniya ta yadda za a raba dukiyar duniya cikin adalci ga dukkan al'ummar duniya.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da bautar zamani, Ayatullah Ramezani ya ce: “Akwai zalunci a duniya da wasu gwamnatoci ke yi wadanda ake iya daukarsu a matsayin bautar zamani da ya kamata a wargaza shi.

 

Iran Ta Zama Ƙasa Mai Ƙarfin Duniya 


Ya ci gaba da cewa: Adalci yana da matsayi mai girma a nazarin Shi'a kuma alamar adalci a cikin wannan nazari shi ne Imam Ali (AS) masu nazari irin su George Jardaq sun kula da wannan lamari. Hankali da ruhi da adalci su ne bangarori uku na Nazarin Tunanin Shi'a da suka samo asali daga koyarwar Ahlul Baiti (AS).

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya kara da cewa: Annabi Isa (AS) zai zo ne domin samar da Ikon al'ummomi. Mu kuma ‘yan Shi’a mun yi imani da cewa Mahdi (AS) zai zo ne domin samar da ikon al’ummomi sannan gwamnati za ta koma hannun salihai kuma wadanda aka zalunta za su yi mulkin duniya, azzalumai, masu girman kai da zasu shafe.

Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya bayyana cewa: Iran ta canja daga mai iko a yankin ta koma mai karfin iko a duniya gaba ɗaya. Karfin da Iran take da shi a fagage daban-daban ya samo asali ne daga ci gabanta da karfin iliminta. A wasu fagagen ilimi, Iran na daga cikin kasashe 10 da ke kan gaba a duniya, kuma tana matsayi na 16 a kimiyance a duniya. Don haka Iran a shirye take ta raba abubuwan da ta samu da kuma nasarorin da ta samu a fannin ilimi ga sauran kasashe. A shirye muke mu samarwa Venezuela abubuwan da muka samu a cikin wadannan shekarun da Iran ta samu a karkashin takunkumin da aka sanya mata.


Shugaban Ƙasar Venezuela Ya Jaddada Girmawarsa Ga Mabiya Mazhabar Ahlul Baiti.


A karshen wannan taro, Ayatullah Ramezani ya bukaci shugaban kasar Venezuela da ya ba da kulawa ta musamman ga mabiya da masoyan mazhabar Ahlul-Baiti a kasar ta Venezuela da kuma gayyatar wakilansu zuwa ga abubuwan da suka dace. Wannan bukata ta samu cikakkiyar kulawar shugaban kasar Venezuela inda ya jaddada cewa a kullum wakilan mabiya mazhabar Ahlul-Baiti mu na gayyatar su.