Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

25 Afirilu 2024

14:23:02
1454015

Ayatullah Ramezani Ya Jaddada Hakan Ne A Ganawar Da Ya Yi Da Ministan Harkokin Wajen Venezuela

A Halin Yanzu Yanayin Gwagwarmaya Ya Bazu A Faɗin Yankin Da Duniya Gaba Daya

Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya bayyana cewa: Guguwar gwagwarmaya ta wuce iyakokin kasar Iran ta kara karfi da fadada zuwa shiyya-shiyya da kuma duniya baki daya ta kuma mamaye zukatan al'ummar duniya duk kuwa da nuna ƙin hakan daga gwamnatoci ma'abuta girman ka.


Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlulbaiti (AS) ya gana tare da tattaunawa da ministan harkokin wajen kasar Venezuela Avon Khel Pinto a ziyarar da ya kai wannan kasa.

A cikin wannan ganawar, bangarorin sun tattauna batutuwan da suka shafi yanayin siyasa da ma'aunin yanayin iko a yankin da ma duniya baki daya, da irin rawar da Iran ke takawa a wadannan ci gaba, da bukatar karfafa mu'amalar kimiyya da fasaha, da amfani da nasarorin da Iran ta samu a wannan fanni karkashin takunkumai kasashen Turai, inda Iran ta zama muhimmin wurin da addinan Ibrahim da tauhidi suke a duniya a yau, wajabcin tattaunawa a tsakanin addinai, da mu’amala da al’amurran musulmi, da ma’abota Ahlul Baiti (A.S) sune lamurran da tattaunawa ta maida hankali a cikinsu.


Iran Ta Kasance Mai Kare Tare Da Goyon Bayan Waɗanda Ake Zalunta A Duniya 


Ministan harkokin wajen kasar Venezuela, "Yon Khel Pinto" a farkon taron, yayin da yake maraba da zuwan Ayatullah Ramezani, ya yi la'akari da babban rikici na tarihi na bil'adama a matsayin sabani ne tsakanin daidai da kuskure, ya kuma bayyana cewa a ko da yaushe Iran ta kasance tana goyon bayan gaskiya kuma tana kare wanda aka zalunta da wanda ake zalunta a duniya.


Ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya kuma taya Iran murnar nasarar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu a baya-bayan nan akan Isra'ila 


Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya da ministan harkokin wajen kasar Venezuela sun tattauna kan gagarumin nasarorin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu a fannin kimiyya da fasaha bayan juyin juya halin Musulunci, tare da yin kokari wajen ganin an cimma nasara don aiwatar da tanade-tanaden yarjejeniyoyin da aka kulla, da kara karfin mu'amalar kimiyya, sun jaddada hadin gwiwar ilimi, bincike da al'adu da amfani da fasahohi da ilimi na kamfanonin ilimi na Iran.

*Tafiyar Gwagwarmaya Ta Mamaye Zukatan Mutanen Duniya 

A wani bangare na wannan taron, Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Baiti (AS), yayin da yake jaddada adalci da neman adalci a matsayin jigon dukkanin addinai na Ibrahim da suka hada da Yahudanci, Kiristanci da Musulunci, ya ce: bisa koyarwar dukkan addinan Ibrahim, bangare ɓata yana rushewa, kuma ɓangaren gaskiya yana mamaye bangaren ɓata ne, kuma ɓangaren da ake zalunta yana samun nasara akan wanda yake zalunci.

Babban magatakardar majalisar duniya ta Ahlul-baiti (AS) ya dauki duniya a yau a matsayin mai kishirwar adalci da ruhiyya tare da jaddada cewa tsayin daka da gwagwarmaya da ake yi a yanzu fiye da iyakokin kasar Iran ya kara karfi da fadada shi a yanki da ma duniya baki daya tare da mamaye zukatan al'ummar duniya duk da muradin kin jinin hakan dafa gwamnatocin ma'abota girman kai.

Ya ci gaba da yin bayani kan asasi na kin jinin zalunci a tsarin ilimi na juyin juya halin Musulunci da Musulunci da kuma mazhabar Ahlul Baiti (a.s) da kuma gabatar da shi a matsayin jigon dukkanin addinan Ibrahim da kuma jaddada matsayin Imam Khumaini (RA) da Jagora wajen Karfafa Bangaren Gaskiya Da kuma jaddada adawa da zalunci.

A bangare na karshe na taron, babban sakataren Majalisar Duniya na Ahlul Baiti (AS) ya bukaci ministan harkokin wajen kasar Venezuela da ya kara ba wa musulmi da magoya baya da mabiya mazhabar Ahlul Baiti (AS) ta kasar Venezuela goyon baya.

Ya kamata a lura da cewa, Dr. Abdul Husain Kalantari mataimakin al'adu da zamantakewa na ma'aikatar kimiyya da bincike da fasaha ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran shi ma ya halarci wannan taro.


...................................