Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti (A.S) - Abna - ya kawo maku cewa: Nazarin rawar da ‘yan Shi’a suke takawa a kasar Palastinu wani bangare ne na tarihi da ba a fadi ba, wanda da wuya kaji an yi magana akan shi. Tarihin kasantuwar ‘yan Shi’a a wannan kasa da kuma arangamar da suka yi da sojojin Rum a yakin Salibiyya don hana mamaye wannan yanki na daya daga cikin wadannan batutuwa.
Ya kamata a fara tarihin Musulunci Qudus tun daga rabin watan Rajab shekara ta 15 bayan hijira, lokacin da aka ci birnin Kudus a karon farko, Khalid Ibn Thabit ya bude wannan yanki a bisa sharadi, sharadin kuwa shine wato filayen wannan kasa na musulmi ne. amma idan dai har Jama'a za su bayar da jiziya to musulmi ba za su tsoma baki cikin lamarinsu ba.
A cikin wannan shekarar ne wasu jama'a daga Madina suka zauna a wannan yanki, kamar Aus, dan kanen Hasan bn Thabit, da wasu sahabbai kamar su Ubada bn Samit. Muawiyah bin Abu Sufyan shi ne gwamnan Qudus na farko kuma ya mulki wannan kasa na tsawon shekaru 40 a matsayin gwamna da sarki ya nada sannan daga baya a matsayin halifan musulmi. Ginin Qubbatus Sakrah shi ne mafi dadewa, mafi kyawu, mafi kyawu kuma mafi daukakar ginin Musulunci a wannan birni, wanda Abdul Malik bin Marwan khalifan Umayyawa na biyar ya gina a shekara ta 72. Watakila wannan gini shi ne aikin Umayyawa daya tilo da ya rage ya zuwa yanzu.
Daga babban ginin masallacin Al-Aqsa, wanda Walid na ɗaya BaUmayye ya gina na tsawon shekaru goma a tsakanin shekara ta 86 zuwa 96, ba a abun yayi saura saboda lalacewar girgizar kasa da sauran illolin da ke tattare da su. An sake gyara wannan ginin sau da yawa kuma mafi yawan abin da ake gani a yau kamar yadda Masallacin Al-Aqsa ya kasance tun daga zamanin Al-Zahir, Halifan daular Fatimidiyya ne.
Hamdaniyawa: 'Yan Shi'a Na Farko Masu Kare Kudus
'Yan Hamdan na daya daga cikin iyalan 'yan Shi'a da ke mulki a Mausul da Halab a karni na uku da na hudu na Hijira. Wannan dangi yana daukar kansa a matsayin dan kabilar Taghlib kuma zuriyar Hamdan bin Hamdun bin Harith bin Lukman Taghlib. Wanda ya kafa gwamnatin Hamdan ta Mausul shi ne Abdullah bin Hamdan. An nada shi gwamnan Mausul a shekara ta 293. A shekara ta 317, Abu Al-Haija ya halarci taron sauke Muqtadar daga kan mulki da nadin Qahir, amma a karshe magoya bayan Muqtadar suka kashe shi.
Bayan rasuwar mahaifinsa Nasarul Dawlah ya ci gaba da zama a cikin gwamnatin yankunan karkashin mulkin mahaifinsa (Mausul da wasu kananan garuruwa) kuma a shekara ta 318 ya zama wakilin Diyar Rabia, Nasibin, Sinjar da wasu yankuna. Bayan 'yan watanni, a shekara ta 318, Muqtadar Abbasi ya mika mulkin Mausul da Diyar Rabi'a ga dan'uwan Abul Haija, Abul Ala Saeed bin Hamdan. Abul Ala ya yaki Rumawa. Da farko ya fitar da Samisat daga kawanyar Romawa. Sa'an nan, ya kama birnin Malatya da yankunan kan iyaka kuma ya dawo tare da ɗimbin fursunoni na Romawa. Bayan Abul Alaa, Nasir al-Dawlah ya fara karfafa tushen mulkin iyalansa a Mausul da kewaye. Zaman mulkinsa ya kasance tare da rigingimu masu yawa da Abbasiyawa da Al-Buyeh har zuwa shekara ta 356.
Muhimmancin da Hamdaniyawa suke da shi wajen kiyaye iyakokin Musulunci da ke kusa da Gabashin Roma, da kuma tabbatar da tsaron cikin gida na yankin Abbasiyawa daga cin zarafin kabilun Kurdawa da Larabawa na tsibirin, ya sanya Abbasiyawa suka yi hakuri suka bar su. Muhimmiyar rawar da Hamdaniyawa suka taka ita ce kare iyakokin yankin Musulunci daga mamayewar Rumawa, kuma an dauki Hamdaniyawa a matsayin babban cikas ga fadada Rum a yankunan musulmi. Don haka a cikin kundin tsarin mulkinsu, wanda kotun Abbasiyawa ta sanar, Jihadi na daya daga cikin muhimman ayyuka na sarkin Hamdani.
Saifud-dawlah ne ya yi jihadi mafi girma a kan Romawa a tsakanin shekara ta 324 zuwa 356, wanda hakan ya sa ya zama ruwan dare abun tsoro ga Romawa. A wasu majiyoyin tarihi, an ambaci yakoki sama da 40 tsakanin Romawa Kirista da Saifud-Dawlah. Yakin da yawancinsu ya shafi mamaye masallacin Al-Aqsa da kasa mai tsarki, sun sanya Hamdani ya zama mafi karfi a yaki da dakarun, kuma an rubuta Saifud-dawlah Hamdani a matsayin wanda ya kasance farkon masu kare Musulunci da Shi'a ga Rumawa.
Hamdaniya Da Buga Tsabar Kudin Na Shi'a
Duk da cewa 'yan Hamdaniyawa sun yi kawance da gwamnatoci da masu iko da Sunna, amma a fili addininsu Imam Shi'anci ne goma sha biyu. An ce Saifud-Dawlah ya fara sauya tsarin al'umma na Halab don goyon bayan 'yan Shi'a ta hanyar daukar matakai tun daga shekara ta 351. Don haka ne ya gina haramomin kaburbura na manyan ’yan Shi’a irin su Amru bin Hameq Khozai, ya sanya sunayen Imamai biyar, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a kan wasu silallan kudin Hamdani.
Kamar yadda Ibn Hauqal ya ruwaito, Abul Haija Hamdani ya gina katanga mai karfi a kewayen kabarin Imam Ali (a.s) kuma ya gina wata babbar kubba da aka lullube da katifu masu tsada a kai. Ibn Adeem ya kuma yi magana game da matakin Saadid Dawlah ya dauka na ƙara jumlar "Hai Ali Khairil-Amal, Muhammadun wa Aliyun Khairul-Bashr" a cikin kiran sallah. Mafi bayyanan alamomin Shi’anci sun bayyana a cikin waqoqin mawaqa na wannan zamani. Abul Firas Hamdani ya sha yabon Ahlul Baiti da zambar makiyansu. Duk da haka, Hamdaniyawa suma suna da sauƙi ga sauran mazahabobin addini.
Sauran Gwamnatocin Shi'a A Ƙasa Mai Tsarki Ta Qudus
Haka nan kuma wata gwamnatin Shi'a mai suna Bani Ammar data kafu a birnin Nablus kuma wanda sun yi yaki da 'yan Salibiyya a Palastinu da Lebanon. Har ila yau, a cikin littafin Ahsanull-Taqasim fi Ma'ra
Ifatul-Aqhalim, na wani masanin tarihi mai suna Maqdisi ya rubuta cewa: "Mutanen Nablus su ma 'yan Shi'a ne" kuma wannan birni yanzu shi ne birni mafi girma a yammacin gabar kogin Jordan. Shi ma Nassir Khosrow Qabadiani ya ambata a cikin littafinsa cewa birnin Tiberias Yan Shi’a ne kuma akwai mabiya Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) acikinsa.
A wasu sassan wannan makala, an yi bayani kan kasantuwar malaman Shi'a a Palastinu da kuma rubuce-rubucen da suka yi a kasar Kudus a tsawon karnoni daban-daban. Yunkurin kusan shekaru dari da malaman Shi'a ke yi na kare kasa mai tsarki da gwagwarmayar kusan shekaru 80 na mahukunta da dattawan Shi'a wajen fuskantar kafuwa da fadada kasar Isra'ila ta bogi shi zai kasance sauran batutuwa da za kunsa nan gaba...