Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

27 Disamba 2024

18:59:55
1517433

Martanin Tel Aviv Game Ga Shugabannin Siriya: Gungun 'Yan Ta'adda Ne!

A yau ne dai ministan harkokin wajen gwamnatin sahyoniyawan ya mayar da martani ga kyamar 'yan tawayen da ke mulkin kasar Siriya inda ya bayyana su a matsayin 'yan ta'adda.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (AS) na kasa da kasa - ABNA - ya habarta maku cewa: Ministan harkokin wajen na wannan gwamnatin ya bayyana shakku game da zaman lafiyar sabuwar gwamnatin Siriya a yayin wani taron aiki a ma'aikatar harkokin wajen kasar inda ya ce sabbin masu mulkin ƙasar Siriya kungiyar 'yan ta'adda ce ba tabbatacciyar gwamnati ba.

Har ila yau ya ce: "Duniya na magana game da sauya tsarin mulki a Siriya, amma abun ba haka ba ne har sai an zabi sabuwar gwamnati ta hanyar dimokuradiyya wacce kuma za ta mullaki dukkan Siriya".

Ya kara da cewa: gungun 'yan ta'adda ne da suka fara a Idlib sannan suka kwace birnin Damascus da sauran wurare kawai.