Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Da yake jawabi a wajen Mauludin Sayyida Fatima Az-Zahra (SA) a ranar Litini 21 ga Jimadat Thani, 1446 (23/12/2024) a garin Abuja, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana lokacin Mauludin Sayyida Zahra a matsayin lokacin murna da farin ciki.
“Haihuwar Sayyida Zahra, ko shakka babu, abin a yi murna ne da shi, saboda Allah Ta’ala ya karrama ta da darajoji masu yawa, ya sa kuma lokacin da ta zo, lokaci ne da ya kamata ya zama abin murna. Har muna cewa, in da da wata rana da za a ce mata ranar mata ta duniya, to ya kamata ya zama ranar haihuwarta ne”. Inji Shaikh Zakzaky.
Jagora ya bayyana yadda daukan cikin Sayyida Zahra ya zama almari na musamman. Yace: “ Kafin a dauki cikinta, sai da aka ce, shi Manzon Rahma (S) ya yi halwa na kwana arba’in, kar ya ci wani abu daga cikin abincin duniya. Don haka ne ma ya tashi daga gidan matarsa Khadija, ya koma gidan uwarsa ta riko; Fatima Bint Asad, ya shiga wani daki ya kulle dakin ba a kai masa abinci, ya kwana 40 a jere baya cin wani abincin duniya, amma yana cin abincin Aljanna”.
Yace: “Mala’ika Jibrilu yana kawo masa abincin aljanna (a tsawon kwanakin). Sai da ya fitar da duk abincin duniyan da ke jikinsa, ya rage ba ko kwarzanen abincin duniya a jikinsa sai na Aljanna. An yi haka nan ne domin ana son a kauwana ruwan da za a yi Sayyida Fatimatuz Zahra da shi, ya zama shi tsantsan ruwan da ya fito ne daga abincin da aka ci daga Aljanna. Saboda haka, lokacin da kwana arba’in ya cika, da ya je ya kwankwasa ma Sayyida Khadija kofa, ta ji sautinsa ta bude, tace kaga ka kara kyau. Shi ma yace ta kara kyau. To shikenan, rannan daren samun Fatimatuz Zahra (SA) ne”.
Da yake bayani dangane da darajojin Sayyida Zahra, Shaikh Zakzaky ya bayyana Fadin Manzon Allah (S); ‘Fadimatu Bid’atun Minni’ da cewa, hakan ya nuna ita Fatima (SA) bangaren jikin Manzon Allah (S) ce. Yace: “ka san kuwa in kace bangaren jiki, ba ka cewa bangaren jiki ya rabu da gangan jiki, bangarensa ne (dindindin).”
Ya cigaba da cewa: “Ba ita Fatima (SA) ba, har ‘ya’yanta ma, alal misali, haihuwar Imam Husain (AS) an ce Ummu Salma ta yi wani mafarki da ya bata tsoro, sai ta yi mafarki an yanko tsokan jikin Manzon Allah (S) an dora mata a cinyarta. Sai ta tashi tana firgice, ta fada wa Manzon Allah (S) ga abin da yake faruwa, ta ga kamar an yanko nama daga jikin Annabi (S) an dora shi a kan cinyarta. Sai Manzon Allah (S) ya yi murmushi, yace abin da wannan ke nufi Fatima za ta haifi da, ke za ki raine shi”.
Jagora yace: “Kun ga ba ma Fatima ba, hatta ‘ya’yan Fatima tsokan jikin Manzon Allah ne. Kun san kuwa tsokan jiki ba ka raba shi da jiki. Inda duk Manzon Allah ya je, nan suke a darajan da yake. Gashi ma a nassin Alkur’ani Allah Ta’ala Yana cewa: “Wallazina amanu wattaba’ahum zurriyatuhum bi imanin alhaqna bihim zurriyatahum wamaa alatnahum min amalihim min shai’in, kullumri’in bima kasaba rahiyna".
“Wanda duk suka yi imani, za mu kai musu zuriyarsu inda duk suke, ba kuma za mu tankware wani abu daga aikinsu ba.” Yace: “Wannan nassin Alkur’ani ne. Ma’ana idan mutum ya yi imani, ya yi aikin kirki, ya shiga Aljanna, sai a debo masa ‘ya’yansa a kawo shi a darajan da yake. Kuma ba rage aikinshi za a yi a ba 'ya'yan nasa domin ya je darajar su ba. Su 'ya'yan ne za a dauko su su kai darajar babansu. Duk masu imani za a yi musu wannan, ballantana Manzon Rahma (S).
“To kun ga Manzon Rahma (S) su wadannan zuriyar tasa suna daidai da shi ne a darajarsa a inda yake a Aljanna –Firdausil A’ala, a nan ne Amirulmuminina yake, a nan Sayyida Zahra take, a nan Imam Hasan yake, a nan Imam Husaini (AS) yake, a nan ‘ya’yan Husaini tara suke. In kace to ya za a yi haka nan? Sai mu ce, haka Allah Ya ga dama. In baka so hakan ba, in ka ji haushi ka mutu”. Inji Shaikh Zakzaky.
Jagora wanda ya bayyana adalci da hikimar Allah Ta’ala akan fifita Manzon Rahma da iyalan gidansa (AS) akan sauran talikai. Yace: “Tun ranar gini ran zane, Allah ya riga ya tsara haka nan, ba bisa hadari ne Allah Ta’ala ya sanya Sayyida Zahra ta zama uwar A’imma ba, wannan an riga an shirya shi ne, ba a nan aka yi ba, ba shura aka yi aka zabe su ba, Allah Ya riga Ya tsara abinSa ne, Ya tsara Sayyida za ta zama sila tsakanin Annabi da Amirulmuminin, ya zama Ausaiya sun fito ta tsatsonta ne".
Ya bayyana Sayyida Zahra (S) a matsayin halitta ta uku a daraja, inda yace: “Mutum daya ne rak a duniya ya cancanci ya auri Sayyida Zahra (SA), shi ne Amirulmuminin (AS), to shi ya fi ta daraja, don daga Manzon Allah sai shi, sai ita, sannan ‘ya’yanta”.
Yace: “Allah Ta’ala bisa hikimarSa, ya so ya zama cewa, ta hanyarta za a gaji Manzon Rahma (S). Da Allah ya so da ya zama Manzon Allah yana da da, sai a gaje shi ta wannan dan nashi, amma sai Allah Ya sanya zai haifi mace ce, -Sayyida Zahra, kuma ya sanya gadon ta hanyarta”.
Bayan kawo wasu daga darajojin Sayyida Zahra (S), Jagoran, ya kuma bayyana jarabawowi da musibu da Sayyida Fatima (SA) ta fuskanta a rayuwarta a matsayin dalilan da suka ahhalata ga samun wadannan darajojin. Inda ya kawo fadin Manzon Allah (S) da ke cewa: “Manya-manyan darajoji suna tare da manya-manyan bala’o’i, kuma tunda Annabawa su ne wadanda suka fi daraja, dole ya zama sun fi kowa shan wahala”.
Jagora ya yi bitan jarabawowin da Annabawan Allah Ta’ala suka fuskanta, musamman Ulul Azmi daga cikinsu. Yace: “Hikima ce ta Allah Ta’ala, Ya shirya cewa, in zai saka maka daraja, sai ya jarrabce ka da wasu jarabawowi domin ka kai ga wannan matsayin".
Ya kuma yi nasiha ga masu dauka ma kansu sai sun yi magana akan abin da ba su sani ba da sunan su Malamai ne. Yace: “Ka’idan hankali da ilimi shi ne, in ka ji abu da baka sani ba, kar kace ba haka bane, domin kasantuwan rashin saninka da abu, ba shi ke mai da abin ba haka ba”.
Sannan ya karkare da tsokaci akan rashin kunyar da jami’an tsaron ‘yan sanda ke yi akan Harkar Musulunci a Abuja. Inda yake cewa: “Na ji an ce shugaban ‘yan sandan Nijeria, Kayode ne sunansa ko mene ne sunansa? Ko ma mene ne sunansa dai, na ji ya fadi cewa wai daga yau ba za mu sake taro a Abuja ba. Shaikh Zakzaky ya ja hankalinsa da cewa: “Kai Mista Kayode, yanzu kai IG ne, amma kafinka an yi IGs, bayanka kuma za a yi IGs, in ka sa kanka a abin da ya fi karfinka kai za mu dora ma alhaki!”
Shaikh Zakzaky kuma ya yi bita akan yadda ‘yan sanda suka tsare ‘yan uwa a makon da ya wuce bayan taron tunawa da ta’addancin Buhari da aka yi a ranar 14 ga Disambar 2024 a Abuja, inda suka kama mota guda akan hanya suka tsare su, sannan suka hana a gansu.
Yace: suna wannan abin ne suna fakewa da cewa sun haramta wata kungiya da suka saka ma suna IMN. Jagora yace: Shugaban kasa na iya cewa ya dakatar da wata kungiya na tsawon kwana 14 a jere, illa iyaka, ba zai wuce haka nan ba. To sai aka rubuta cewa an yi banning wata kungiya IMN, aka ce kuma Abba Kyari ya saka hannu, alhali bashi da ikon yin hakan'.
Yace: “Na fada wa Lauyanmu Falana, nace, ai bamu da wata kungiya sunanta IMN. Sai yace, a manta da wannan ma, a dokance ba su da ikon su hana. To ballantana, mu muna amfani da kalmar Islamic Movement ne a matsayin ideology, kamar mu ce Islamic education, ko Islamic awareness, ko wani abu mai kama da haka nan, amma ba sunan wata kungiya ce ba, ko ina a duniya akwai Islamic movement, yana nufin mutanen da suke motsin Musulunci.
“Shekaranmu arba’in da ‘yan kai, galibanku wadanda kuke ‘yan sanda din nan duk muna Harkar nan lokacin duk kuna firamare, wasu suna sakandire, mafi yawan ‘yan sanda ma ba a haife su ba. Muna abinmu, yau shekara sama da 47, sai rana daya ku zo ku bamu wani suna wai kun bamu wani suna (wai IMN, kuma wai) an yi banning dinmu.
“Muna da dukkan hakki, mun san kuma hakkinmu. Ina fadin wannan ne domin yanzu, kamar yadda suka yi mana wancan makon (suka kama wasu ‘yan uwa bayan an tashi taro), suna ganin za su cigaba da yi ne, kuma lallai abinda muke ba su tabbacin cewa, duk abin da muke yi ba wanda za mu fasa!
“A lokacin mulkin Buhari ba abinda bai yi ba, ba kuma abin da ya hana! Haka nan kowane ma in ya zo zai yi ya gama. Iyakanka IG ne, shekara nawa ne? Maigidan naka shi ma shekara nawa zai yi? Zai zo ya wuce ne! An yi wasu IG kafinka, kuma bayanka ma za a yi wasu. IG ba mutum ba ne, ofis ne, kai kake ciki, watarana kuma wani ne zai zama a cikinsa. Saboda haka ka yi aikin da ya dace da kai a yaba maka, ko kuma ka yi abin tsiya a soke ka a kai. Wannan kuma nasiha ne.” Ya karkare.
A karshen jawabinsa, Shaikh Zakzaky ya yi fatan Allah Ya maimaita mana Mauludin Sayyida Zahra a shekaru masu yawa. Tare da addu’ar Allah Ya kara mana son Annabi da son iyalan gidan Annabi (S), Ya kuma raya mu, ya dauki rayukanmu, mu zauna a kabari, mu tashi a tafarkin iyalan Annabi (S) ya gamar da da su a gidan tsira.
SZakzakyOffice
21/Jimada Ath-Thaniyah/1446
23/12/2024