Sanarwar Sojin Tsraon Sama Iran Dangane Da Harin Da Isra’ila Ta Kai Kasar A Daren Jiya:
Duk da gargadin da jami'an Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka yi a baya
ga mahukuntan haramtacciyar kasar Isra'ila sahyoniyawa masu aikata muggan
laifuka da su guji duk wani yunkurin tsautsai na kawo hari, amma a safiyar yau
ne wannan gwamnatin ta bogi ta kai hare-hare kan wasu cibiyoyin soji a lardunan
Tehran da Khuzestan da kuma Ilam tare da nasarar tunkarar hadakar tsarin tsaron
sama na kasar kare wannan ta'addanci, an yi barna kadan a wasu wurare, ana kan
bincike kan girman wannan lamari.
Dangane da haka, yayin da hakan ke faruwa awanna yanayi ana jan hankalin Al’umma wajen bada hadin kai don wanzar da hadin kai da zaman lafiya, an kuma bukace su da su rika bibiyar labaran da suka shafi wadannan al'amura ta kafafen yada labarai na kasa, kada su kula da jita-jita na kafafen yada labarai na makiya.