Tare da halartar jami'ar Tehran; A
safiyar yau Alhamis Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali
Khamenei ya halarci jami'ar Tehran inda ya yi sallah ga gawar shahidi Ismail
Haniyyah shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas da shahidi Wasim Abu
Sha'aban wanda yayi masa rakiya kuma sukai shahada tare.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku cewa: a safiyar yau Alhamis ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya halarci jami'ar Tehran inda ya gabatar da sallah da addu'o'i ga gawar shahidi Isma'il Haniyyah shugaban ofishin siyasa na Hamas da kuma abokin rakiyarsa shahidi Wasim Abu Shaaban.
An gudanar da taron sallar ne tare da halartar dimbin jama'a daga sassa daban-daban, jami'an kasa da na soji, da iyalan shahidi Ismail Haniyyah da kuma wata gungu na yan gwagwarmayar Musulunci ta Palasdinu da Lebanon.
Bayan gabatar da Sallar Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gana da iyalan Shahidai Isma'il Haniyyah da kuma jami'an gwagwarmayar Musulunci na Palastinu tare da jajanta masu.




