Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku cewa:
Musulman birnin Frankfurt na kasar Jamus sun gudanar da zanga-zangar nuna
rashin amincewarsu da rufe cibiyar muslunci ta birnin Frankfurt da mahukuntan
Jamus suka yi, inda suka gudanar da sallar Juma'a a gaban cibiyar Musulunci ta
wannan birni.
Tare da rike da allunan masu dauke da rubutu mahalarta taron sun yi Allah wadai da rufe cibiyoyin Musulunci a Hamburg da Frankfurt da kuma Berlin da gwamnatin Jamus ta yi, wanda wani mataki ne na takaita 'yancin addini na musulmi a wannan kasa.
Musulman birnin Hamburg na kasar Jamus sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da rufe cibiyar muslunci ta birnin Hamburg da gwamnatin Jamus ta yi a jiya inda suka gudanar da wani gangami a gaban cibiyar Musulunci ta wannan birni.
Idan dai ba a manta ba a ranar Laraba 24 ga watan Yuli ne kafafen yada labaran Jamus suka bayar da rahoton cewa, jami'an 'yan sandan kasar sun kai hari a cibiyar Islama ta Hamburg da wasu cibiyoyin addinin musulunci da ke da alaka da ita, sannan kuma daga aka ftar da sanarwar cewa an haramta ayyukan wadannan cibiyoyi. A cikin wannan yanayi, ma'aikatar harkokin cikin gidan Jamus ta sanar a cikin wata sanarwa cewa ta haramta ayyukan cibiyar Islama ta Hamburg da cibiyoyinta a biranen Frankfurt, Munich da Berlin saboda bin manufar 'yan kishin Islama. Sakamakon wannan haramcin, za a rufe masallatai 4 na mabiya Shi'a a Jamus tare da kwace kadarorin cibiyar Musulunci ta Hamburg.







