Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: a taron kasa da kasa na Imam Riza (a.s) da aka fara a ranar Litinin 13 ga watan Mayu da an bude taron da sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma an gama taron a yammacin jiya Talata da jawabin shugaban Iran Dr. Sayyid Ibrahim Raisi.
A karshen wannan taron bikin, an mika wa shugaban kasar Hojjat-ul-islam Wal-Muslimin Sayyid Ebrahim Raisi, Mushafin Mashhad Razawi wanda yake da tsufan shekaru 1,200 da shugabanni masu kula da Haramin Quds Razavi su ka yi.
Mushaf Mashhad Razawi shi ne mafi cikar kammalalle kur’ani da aka rubuta a cikin rubutun Hijazi daga karni na farko na Hijira, wanda ya cika shekaru 1,400 kuma aka gabatar da kyautar shi ga shugaban kasar Iran.
Yana da kyau a bayyana cewa littafin Mushaf Mashhad Razawi mai shafuka 252, shi ne mafi cikar takardu daga cikakken kur’ani tun karni na farko na Hijira, wanda ya kunshi fiye da kashi 95% na nassin kur’ani Mushaf na Mashhad Razavi ya samo asali ne tun rabi na biyu na karni na farko na Hijira bisa ingantacciyar dangantaka a dakunan gwaje-gwaje na duniya.
Wannan Mushafi ne mai daraja mai suna "Mushaf Mashhad Razawi" tare da cikakken bincike da gabatarwa mai zurfi an buga shi a shekara ta 1402 tare da ƙoƙarin kulawar Haramin Quds Razawi da Cibiyar Al-Bait Ihya Al-Trath a cikin nau'i na fakitoci.
Yana da kyau a faɗi cewa ainihin sigar Mushafin Razawi yana cikin Cibiyar Rubuce-rubuce na gungun Laburaren Gidajen tarihi da Cibiyar Dakin ajiye littattafai na Ustan Quds Razawi.