Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

11 Mayu 2024

11:04:41
1457710

Ta Ya Murna Da Ranar Haihuwar Sayyidah Fatimah Ma’asumah Karimatu Ahlul Bayt As (01/11/173H)

A lokuta da dama masoya da masu kaunar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) su kan yi ta murna da farin ciki bisa wata muansa ta murna daga cikin farin cikinsu har da maulidodi masu albarka: Kuma a cikin wadannan ranaku da muke ciki muna cikin gayar jin dadi da murna na haihuwar mace mai daraja (Fatimatul-Ma’asumah (amincin Allah Ta'ala da amincin Allah su tabbata a gare ta)) wacce aka haifeta a ranar daya ga watan Zul Qa’adah shekarata 173H.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Muhammadu tare da alayensa tsarkaka, da la'ana ta tabbata ga makiyansu har zuwa ranar sakamako...

Bayan Haka.

A lokuta da dama masoya da masu kaunar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) su kan yi ta murna da farin ciki bisa wata muansa ta murna daga cikin farin cikinsu har da maulidodi masu albarka: Kuma a cikin wadannan ranaku da muke ciki muna cikin gayar jin dadi da murna na haihuwar mace mai daraja (Fatimatul-Ma’asumah (amincin Allah Ta'ala da amincin Allah su tabbata a gare ta)) wacce aka haifeta a ranar daya ga watan Zul Qa’adah shekarata 173H.

Sayyidah Fatima Al-Ma’asumah (amincin Allah ya tabbata a gare ta) diyar Imam Musa Al-Kazim (amincin Allah ya tabbata a gare ta) ce. Tana da matsayi mai girma a cikin imamai, kuma an samu ruwayoyi game da ita da suke nuni da hakan.

Haihuwarta:

Saboda irin yanayin mai tsanani da da hukumar Abbasiyawa ta haifar wa Imam Musa Al-Kazim, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi wuya a iya tantance ainihin ranar da aka haifi Sayyidah Ma’asumi, don haka ne ma wasu marubuta suka ambata cewa haihuwarta, tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta, ta kasance a shekara ta 183, wato shekarar da mahaifinta Imam Al-Kazim ya yi shahada, kuma wannan shi ne ra'ayin mafi yawan malaman tarihi (1).

Don haka, Sayyidah Ma’asumah ba ta samu damar saduwa da mahaifinta, Sallallahu Alaihi Wasallama da kulawarsa ba, sai ta zauna a qarqashin kulawar da dan uwanta, Imam Reza, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Wasu mawallafa sun kore yi wuwar ya zamo a wannan shekarar ne aka haife ta, domin kuwa shekaru hudun karshe na rayuwar Imamul Kazim, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a lokacin yana a cikin gidajen yari Abbasiyawa (2).

Yayin da wasu kuma suka ce haihuwarta – Salamullahi Alaiha ta kasance a farkon watan Zul-qi’da na shekara ta 173 bayan hijira (3).

A bisa wannan tarihin, Sayyidah Fatima ta zauna tare da mahaifinta na tsawon shekaru goma, amma a cikin shekaru hudu na ƙarshe na rayuwarsa, hukumar Abbasiyawa ta lokacin ta kamashi ta sanya shi a gidan yari, kenan ta sami shekaru shida kawai na lokacinsa a rayuwarta.

Sunayenta da Lakubbanta Salamullahi Alaiha

Yayin da ya kasance sayyidah Ma’asumah ta zamo ta kasance diya kuma tarbiyar Imamai As, ta samu mafificin sunaye da mafi kyawun lakubba, kuma sunaye da lakubbanta suna da ma’anoni da suke nuni da irin matsayinta da Daukakarta a idanuwan Imamai, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su:

Ga wasu daga bayanin sunayenta:

1. Fatima

Duk wanda yake bibiyi rayuwar iyalai tsarkaka, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, ya san abun da wannan suna ya kebanta da shi ta yadda Imamai, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, suka ba wa wannan suna muhimmanci, wanda ba mu samu irinsa ba ga sauran sunaye.

2. Ma'asumi

Wannan suna yana gwame da sunan Fatima ‘yar Imam Musa bin Jaafar, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, don haka a mafi yawan magana ana cewa: Fatima Ma’asumi, kamar yadda ake cewa a wajen ambaton babbar mahaifiyarta: Fatimatuz  Zahra Alaiha Salam.

An ambaci wannan suna a cikin wata ruwaya daga Imam Ali Ar-Rida, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, inda yake cewa: “Duk wanda ya ziyarci ma’asumi a Kum, to kamar wanda ya ziyarce ni ne” (4).

Wannan suna yana nuni da cewa Sayyida Fatima (amincin Allah ya tabbata a gare ta) ta kai kurewar matsayin madaukaka na kamala, da falala, Domin Isma tana nufin: (tsarewa da kariya, kuma ma'asumi shi ne wanda ya nisanci dukkan abubuwan da Allah Ta'ala ya haramta. ma'ana: Isma bata cin karo da zabi, don haka matakin kamala ne wanda rai ta hanyar shi bata iya yunkurin aikata zunubi balle a ce ta aikata shi da ganganci, ko bisa kuskure, ko da mantuwa, kuma bai zamowa ta saba wajen aikata daya daga cikin wajibai, ko ma sabawa a matakin farko ne, kamar yadda ya ke ga iyalan gidan manzon Allah sallallahu alaihim wa sallam. Kuma it aba wai lamari ce na bayyane ba sai dai ita wani yanayi ce na boye daga yanayin rai kuma ana kafa hujja ne da ita da nassi ne, ko kuma tabbatacciyar hujjar da ke tabbatar da ingancinta, kuma tana da matakan da iko da dabi’u da suka bambanta daga wani mutum zuwa wani (5), kamar misalin ma’asumancin Sayyida Zainab da ma’asumancin Abul-Fadl Abbas Alaihimussalam.

3. Karimatu Ahlul Bayt As

Yana daga cikin lakubban da aka kebance wannan baiwar Allah da shi, kuma ta shahara da shi koma bayan sauran matan Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su.

Haka nan Imam Al-Hasan Al-Mujtaba, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya shahara a gabanta da wannan lakabin sama da sauran mazaje, don haka ake kiransa da Mafi karamcin Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su.

(Imamul-Hujjah ya ba ta, Allah Ta’ala ya gaggauta bayyanarsa mai daraja, a cikin wani labari da ya faru da daya daga cikin ma’abota daraja (6) sai ya ce masa: “Lallai ka kaje wajen Karimatu Ahlul Bayt” yana nufin wannan baiwar Allah (7).

Tafiyar ta As zuwa Kum

Wannan lakabi yana da ma'ana mai zurfi dangane da matsayin Fatima 'yar Imam Musa bn Jaafar, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, domin Ahlul-Baiti, Sun tattaro mafi kyawun sifofi da kyawawan halaye da kyawawan matsayi. kuma daya daga cikin fitattun sifofin nan shi ne karamci, masana harshe sun siffanta shi da cewa: (fifita wasu da kyautatawa, kuma Larabawa ba sa amfani da wannan kalma sai dai a mafi wajen kyautatawa da yawa, kuma ba a ce mutum mai karamci har ya bayyana daga gare shi)  (8) Mai karimci shi ne wanda ya tara dukkan nau'ikan alheri da daraja da kyawawan halaye.

Daga nan ne aka san cewa karamci yana da ma’ana mai fa’ida wadda ba ta takaitu ga bayar da kudi, ko girmama bako ba, domin wadannan misalai ne na karamci ba cikakkiyar ma’anarsa ba. Bisa dogaro da wannan cikakkiyar ma’anar karamci, zai bayyana mana abin da ake nufi da siffanta Ahlul-Baiti, Sallallahu Alaihi Wasallama a matsayin mutanen da suka fi kowa kyauta saboda nau’ukan alheri da daraja da kyawawan halaye da suke da su. kuma tarihi ya adana mana wasu daga cikin haka kuma maruwaita sun ruwaito shi. Haka nan ya tabbata a gare mu cewa wannan baiwar Allah ita ce mai martabar matsayi na Karimatu Ahlul Bayt As.

Daya daga cikin fitattun abubuwan da ke nuni da karamcinta shi ne, wurin makwancinta mai tsarki wanda ya kasance har yanzu shi ne mabubbugar wadata, mafaka ga mutane, mafakar masu ibada, mafakar halitta, kuma kofar rahamar Ubangiji ga masu neman ta.

Shaikh Saduq ya ruwaito da isnadinsa daga Makhawl Sijistani, ya ce: “Lokacin da mai kawo wasiku ya zo da takardar kiranyen Imamur Rida, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, zuwa Khurasan, na kasance a Madina, sai ya ya shiga masallaci don yin bankwana da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa yayi bankawana da shi sau da dama, duk zuwan da zayyi wajen kabari yana daga murya da kuka. sai na matso na gaishe shi, sai ya mayar da gaisuwata na taya shi murna. Sai yace:

"Ka ziyarce ni, domin zan bar kusan kakana, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa, kuma zan mutu ina mai hijira za’a rufe ni kusa da Haruna" (9).

Sai Imam Rida, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tashi ya tara iyalansa, ya umarce su da yi masa kuka, don ba zai koma wurinsu ba, sai suka yi masa zaman makoki kafin ya yi tafiya zuwa Khurasan (10).

Fitar Imam Rida (a.s) daga Madina shekara ta 200 ne, kuma shahadarsa ta kasance a shekara ta 203 bayan hijira  As (11). Amma fitar daga madina domin taje wajensa  ya kasance a shekara ta 201 bayan hijira, ayarin mutane ashirin da biyu suka fita tare da ita, da suka hada da ‘yan’uwa, da ‘ya’yansu, da bayi (12).

A lokacin da ayarin suka isa Sawa, sai mutanen Al-Ma’amun suka yi musu kawanya, suka kashe duk wanda za su iya, sauran suka waste, kuma sun jiwa wa Haruna dan’uwan Imam Rida, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ciwo. Kuma babu wanda yayi saura a tare da ita said an uwanta Haruna, wanda ya samu rauni, shima sai suka farmakeshi yana cin abinci, suka kashe shi (13).

Dukkn Wannan ya kasance a akan idon Sayyidah Fatima Ma’asumah, amincin Allah ya tabbata a gare ta, ta ga yadda aka kashe 'yan'uwanta da 'ya'yansu, kuma ta ga irin gudun hijirar wadanda suka rage a lokacin? Don haka sai ta yi rashin lafiya saboda hakan, a wata maganar kuma ance: An sanya mata guba a cikin Sawa, sai ta yi rashin lafiya saboda haka Sai ta umurci wani bawanta da ya dauke ta zuwa Kum, a lokacin da mutanen Kum suka ji labarin tahowarta zuwa Kum, sai suka fita domin tarbar ta, a karkashin jagorancin Musa bin Khazraj Al-Ash'ari, kuma ya samu karramawar bakuncinta, ta zauna a gidansa har tsawon kwanaki goma sha bakwai, sannan ta rasu, a ranar goma ga watan Rabi'ul- Thani.

Falalar ziyartarta, Salamullahi Alaiha.

An ruwaita a cikin ruwayoyi masu yawa dangane da umwarni da zuwa ziyararta, Salamullahi Alaiha, da kuma cewa Allah Ta’ala ya sanya Aljanna ta zama lada ga duk wanda ya ziyarce ta, kuma daga cikin ruwayoyin akwai:

Na farko: Mutane da yawa daga garin Ray sun je wajen Abu Abdullah As-Sadik, amincin Allah su tabbata a gare shi, suka ce: “Mu mutanen Ray ne, sai Imam As ya ce:

"Sannunku da zuwa 'yan'uwanmu daga mutanen Kum."

Sai suka ce: Mu daga mutanen Ray ne, sai ya maimaita maganar, sai ya ce:

“Allah yana da harami, shi ne Makka, kuma Manzo, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa, yana da harami, shi ne Madina, kuma Amirul Muminin, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana da harami wadda shi ne Kufa, kuma mu muna da harami, wato garin Kum, kuma a can za a binne wata mata daga cikin ‘ya’yana Fatima, don haka duk wanda ya ziyarce ta za a ba shi Aljannah”.

Mai ruwaya ya ce: Wadannan kalmomi sun zo daga gare shi tun kafin a haifi Al-Kazim, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (16).

Na biyu: Abin da Shaikh Saduq ya riwaito da isnadinsa daga Saad bin Saad, wanda ya ce: “Na tambayi Abul-Hasan Ar-Rida, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, game da Fatima ‘yar Musa bin Ja’afar, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, sai ya ce: ‚Wanda ya ziyarce ta yana da Aljannah” (17).

Na uku: Abin da aka ruwaito daga Saad daga Imam Aliyu bin Musa Ar-Rida, As ya ce: “Ya Saad, muna da kabari a wajenku” sai n ace: “kai kabarin Fatima ‘yar Musa As, sai ya ce: “Na’am, duk wanda ya ziyarce ta yana sane da matsayinta Aljanna ta wajaba a gare shi” (18).

Na hudu: Abin da kuma aka ruwaito daga gare shi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Duk wanda ya ziyarci ma’asumi Qum, kamar wanda ya ziyarce ni ne” (19).

Na biyar: An karbo daga Abu Ja’afar Muhammad bin Ali Al-Jawad As, ya ce: “Duk wanda ya ziyarci kabarin goggona a Kum, yana da Aljannah” (20).

Karamominta As:

Sayyida Abul-Fadl Razawi Zadeh, daya daga cikin masu yiwa Sayyidah Ma’asumah, amincin Allah ya tabbata a gare ta hidima, ya nakalto daga wani abokinsa na hidima, yana mai cewa:

A farkon isowar Ayatullahi Sayyid Al-Mar’ashi Al-Najafi Allah Ya yi masa rahama daga Najaf Al-Ashraf mai girmama zuwa Kum, yana cikin damuwa matuka, domin da yawa daga cikin masu neman diyarsa da uare sun fito domin neman auranta, amma saboda tsananin halin rashi da yake ciki, ya kasa samun wadatar yi mata kayan aure, sai watarana ya zo Harami ya yi wa Sayyidah Ma’asuma As yayi munajati da ita ya ce: ya Sayyidaty! Me ya sa ba za ki yi tausayamin ki dubi halin da nake ciki ba? Bayan yayi hakan, sai ya ga a cikin mafarki wani daya daga cikin masu hidima ga Sayyidah Ma'asuma, aminci ya tabbata a gare ta, ya ce masa: Sayyidah Ma'asuma, Amincin Allah ya tabbata a gare ta, tana neman ka.

Sai Marigayi Al-Marashi ya cewa game da wannan mafarkin nasa: “A duniyar mafarki, na samu dacewar ziyartar Sayyidah Ma’asuma, Amincin Allah ya tabbata a gare ta (nan take), kuma a lokacin da nake son shiga Wuri Mai Tsarki da Kubbar Azurfa (tsohon ginin) sai na ga mata guda biyu suna shara, kuma daya daga cikinsu ita ce Sayyidah Fatima Al-Zahra, amincin Allah ya tabbata a gare ta, kamar yadda na gan ta a mafarkin da ya gabata, dayar kuma ita ce Sayyidah Ma'asuma, amincin Allah ya tabbata a gare ta, kamar yadda ta ke, yayin da ta kasance mafi kankanin jiki fiye da Sayyidah Fatima Al-Zahra, amincin Allah ya tabbata a gare ta.

Ta ce da ni: Ya Shihab! Kuna karkashin kulawa da kiyayewar mu, don haka kada ka damu a duk inda kake, ko a Najaf ko Kum.

Sayyid Al-Marashi Al-Najafi, Allah ya yi masa rahama yana cewa: Daga qarshe yanayina da rayuwata sun inganta tun daga wannan rana, suna qara samun inganta qwarai (21).

Madogara:

 

(1) A’alamun Nisa’il  Mu’uminat: shafi na 576.

(2) Karimatu Ahlulbaiti As: shafi na 103.

(3) Mustadrak Safinatul-Bahar: juzu'i na 8, shafi na 261.

(4) Riyahinush -Sharia: juzu'i na 5, shafi na 35.

(5) Fatimatul –Ma’asuma na Muhammad Ali Al-Muallem: shafi na 68-69.

(6) Shi ne Sayyid Mahmoud Al-Marashi, mahaifin Ayatullahi Shihab Al-Din Al-Marashi, Allah Ya yi masa rahama. (Karimatu Ahlulbaiti, As: shafi na 43; Sayyidatu Ush Ali Muhammadu, Alaiha Salam: shafi na 35-37.

(7) Fatimatul –Ma’asuma na Muhammad Ali Al-Muallem: shafi na 74-75.

(8) Majama’ul Bahrain: Kashi na 6, shafi na 152.

(9) Uyun Akhbar Al-Rida: juzu'i na 2, shafi na 217.

(10) Uyoun Akhbar Al-Rida: Part 2, shafi na 217-218.

(11) Muntaha Al-Amal: juzu'i na 451 da shafi na 499.

(12) Alhayatus Siyasiyyatul Imam Rida As, na Sayyid Jaafar al-Amili: shafi na 428.

(13) Hayatul Imam Al-Rida As, na Sayyid Jaafar Murtada Al-Amili: shafi na 428, cirow daga Jami’ Al-Ansab: shafi na 56.

(14) Alhayatus Siyasiyyatul Imam Rida, Amincin Allah ya tabbata a gare shi: shafi na 428.

(15) Tarikh Qum: shafi na 213.

(16) Tarikh Qum: shafi na 215. Bihar Al-Anwar: juzu'i na 60, shafi na 216-217.

(17) Uyun Akhbar Al-Rida: juzu'i na 2, shafi na 267.

(18) Bihar Al-Anwar: juzu'i na 99, shafi na 266.

(19) Riyahin al-Sharia: juzu'i na 5, shafi na 35.

(20) Kamil Al-Ziyarat: Babi na 106, Falalar ziyarar Fatima bint Musa bin Jaafar, amincin Allah ya tabbata a gare su: Hadisi na 2, shafi na 536.

(21) Hayatu Wa Karamatu Fatima Al-Masuma As na Al-Buqa’i: shafi na 117.