Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewaa: Sanatoci 12 na jam'iyyar Republican sun yi wa babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya barazana a wata wasika cewa bayar da sammacin kama Netanyahu zai yi mummunan sakamako a kansa da iyalansa da ma'aikatansa! Hakan ya biyo bayan yukunrin babbar kotun koli na bada sammaci ga Netanyahu da mukarrabansa. Inda suka sanya hannun akan wannan mummunan kudiri domin hana yanke hukunci ko ci gaba da gudanar da karar da aka shigar domin ganin an samawa Falasdinawa yan cin kansu tare da hukunta Isra’ila akan munanan laifukan yaki da aikata akan al’ummar Falasdinu.
Madogara : ابنا
Laraba
8 Mayu 2024
05:46:26
1457022

Sanatoci 12 na jam'iyyar Republican sun yi wa babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da iyalinsa barazana