Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

6 Mayu 2024

18:20:19
1456633

Jiragen saman Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a yankuna 2 na Rafah.

"UNICEF" Tayi Gargadi Game Da Bala'in Harin Da Ke Gabatowa Ga Yara Falasdinawa 600,000 A "Rafah"

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadi game da wani sabon bala’i da ke shirin afkuwa kan yara sama da dubu 600 a wannan birni a yayin harin da ‘yan mamaya zasu kai kan birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya yi gargadi game da wani sabon bala’i da ke shirin afkuwa kan yara sama da dubu 600 a wannan birni a jajibirin harin da ‘yan mamaya suke son kai wa birnin Rafah dake kudancin zirin Gaza. Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya jaddada ta hanyar buga wata sanarwa cewa, dimbin yaran Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a birnin Rafah na cikin wani mawuyacin hali.

UNICEF ta kuma sanar da cewa, saboda mashigar da ake yi bi wajen jigilar mazauna birnin da ‘yan gudun hijira daga Rafah, cike ya ke da nakiyoyi da alburusai, ba a tashe su ba, sannan kuma babu shiryayyun wurare da aka samar a yankunan da aka nufa, da yiyuwar wani sabon bala'i zai faru ga yara.

Wannan kungiya mai alaka da Majalisar Dinkin Duniya ta yi nuni da cewa harin da sojojin Isra'ila suke son kaiwa kan Rafah na iya haifar da mutuwar fararen hula da dama da kuma lalata bangaren hidima da kuma kayayyakin more rayuwa da ake bukata don samar da wadannan ayyuka.

Catherine Russell, darektan asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, ta ce yanzu Rafah ta zama birni na yara, kuma yara a wannan birni ba su da inda za su fake a zirin Gaza. Idan aka fara wani gagarumin aikin soji, yara ba wai kawai za su fuskanci hadarin fuskantar tashin hankali da yaki ba, har ma da rudani da fargaba. Wanda a halin da ake ciki dai yanzu sun jinkunansu sun gaji da tunaninsu saboda yanayin yaki a zirin Gaza.

UNICEF, wacce ta sake yin kira da a tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ta jaddada cewa kimanin jarirai 78,000 ‘yan kasa da shekaru 2 da kuma yara 175,000 ‘yan kasa da shekaru biyar (90% na yara) a Gaza suna fama da wata cuta ko fiye da haka.

A halin da ake ciki kuma, hukumar kare fararen hula da kuma kungiyar agaji ta Red Crescent na zirin Gaza sun sanar da cewa: Jiragen saman Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a yankuna 2 na Rafah.