Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

4 Afirilu 2024

18:51:27
1449104

Jawabin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Na Nuna Goyon Bayan Al'ummar Palasdinawa A Ramadan 1445 (2024).

Domin Dole Ne Mu Zama Masu Taimakon Wanda Ake Zalunta, Mu Yi Fada Da Wanda Ke Zalunci. Ko Ma Meye Addininsu, Ko Da Addininsu Wani Irin Addini Ne Ba Irin Namu Ba, Ma’ana Ko Da Su Ba Musulmi Ba Ne.

              Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya kawo maku bayanin Shekh Ibrahim Ya’aqub Alzakaky Shugaban Harkar Musulunci A Najeriya anda ya gabatar bisa nuna goyon baya ga Al’umma r Falasdinu da ake Zalunta bisa zagayowar ranar Qudus ta duniya wanda za’a gudanar da tarukan a fadin duniya a gobe Juma’a 26 ga watan Ramadan bisa kidayar Najeriya 25 kidayar Iran.

Taimakon Raunana:

                To kuma, mu a wurinmu, lallai addini ne, don a sani, lallai addini ne. Amirulmuminin (AS) yana cewa “Kunu lil mazlumina aunan, wa liz zalimina kasma.” “Kunu kasman liz zalimina, wa lil mazlumina auna.” Ma’ana, ku kasance masu fada da azzalumi, masu taimakon wanda ake zalunta. Wajibi ne cikin wajibobin addini. Manzon Allah (S) yana cewa “Man lam yahtamma bi amril Muslimina falaisa minhum.” “Man ashaba walam yahtamma bi amril Muslimina falaisa bi Muslimin.” Wato, wanda ya wayi gari bai damu da abin da ya shafi Musulmi ba, bashi a cikinsu.

                Kuma Manzon Allah (S) ya kamanta al’ummar Musulmi da tamkar jiki daya, wanda in wani bangare aka taba shi sauran jiki na amsawa da rashin lafiya. Ba yadda za a yi idan ido ke ciwo yatsa yace ba ruwansa, ko in yatsa ke ciwo na ciwo ido yace ba ruwanshi. In yatsa ke ciwo ido ya shiga yin ruwa kenan, ba zai kuma yi bacci ba, saboda duk inda ka taba a jikin mutum, duk sauran jikin zai amsa. To haka ya kamanta al’ummar Musulmi. Saboda haka in aka taba wani bangare na al’ummar Musulmi ka ji kai baka ji ba, to baka a jikin, ko kuma ka mace. Don idan wani bangare a jikin mutum ya mace, ko an soka allura ba zai ji ba, in bai ji shigan allura ba, yana nufin wannan bangaren ya mace, ya tashi a jikinsa, ya zama wani abu daban.

                To, wanda duk yake ganin abin da ke faruwa yanzu a Falastinu, ya zama shi abin bai dame shi ba, alal akalla ko da ace masallatai, wanda ban san yanzu ko sun kai masallaci nawa ba? Akwai lokacin da aka ce, sun rusa masallaci manya-manya wanda ake sallar Juma’a guda 58, kuma wani lokaci suna rusa masallatan nan akan masallata ne. To ko da wannan ne, kana Musulmi, bai kamata ya dame ka ba?

                To ballantana ma mu duk inda ake zaluntar wanda ake zalunta, ko meye addininsa, mu dole mu damu. Domin dole ne mu zama masu taimakon wanda ake zalunta, mu yi fada da wanda ke zalunci. Ko ma meye addininsu, ko da addininsu wani irin addini ne ba irin namu ba, ma’ana ko da su ba Musulmi ba ne.

Game Da Matsayar Gwamnatin Nijeriya Akan Al'amarin Palasdinawa

                “To mahukunta kuma, zan karkare magana da su, don su mahukuntan kasar nan su basu damu ba, ko kalma guda ba su yi ba dangane da abin da ke faruwa a Palasdinu. Ko kalma guda bamu ji daga gare su ba, illa iyaka wasu an ce sun taba cewa wai suna goyon bayan a yi kasa biyu, wai ‘two states solution’.

                “Ba yadda za a yi kasar mutum wani ya kwace, kazo kace a raba. Wani ne yake da abu, sai wani ya je ya kwace, yace nasa ne, sai kace yanzu don a zauna lafiya a raba a ba kowa nashi. Wannan adalci ne? Me abu ake ba abinsa. Kasa ta Palasdin ce, babu wata kasa wai sunanta Isra’ila.

                “Kuma Isra’ila za ta gushe, dama kafata aka yi da karfin tsiya, kuma za ta gushe, tana kan kuma hanyar gushewa ne. Ba batun wani abu wai shi ‘two states solution’. ‘Solution’ din shi ne Palastine ya zama na Palasdinawa. In wani mutum sunansa Bayahude ne shi, ko Ba’isra’ila ne shi, yana iya zama a cikin kasar Palasdinu lafiya lau a matsayin Bafalasdine, ko kuma ya zauna a matsayin dan gudun hijira, in an bashi mafakan siyasa. Amma ba zai yiwu a yi kasa biyu ba. Ba yadda za a yi wani ya kwaci kayan wani, ace su raba. To iyaka abin da muka ji daga hukuman Nijeriya kenan.

                “Kamar yadda nake faɗi, ko ‘yan watannin baya sai da suka yi harbi (a Nijeriya). Kuma sun gwada mana su a shekarun nan, in dai mu ne, ko ma me muke yi suna harbi ne. To kuma mun sha fada musu, za mu kuma sake maimaita musu; Kar su dauka in sun yi harbi za su hana wani abu, domin ba abin da za mu fasa. Ko a yi harbi, ko kar a yi harbi, ko a goyi baya, ko kar a goyi baya, za mu cigaba da abinmu.

                “Mu muna ganin abin ya shafe mu, namu ne! wanda suke cewa, ku me ya hada ku da Palasdinawa? (Su sani) Duk cikanmu Palasdinawa ne! Kuma duk cikanmu mu ake zalunta! Kuma muna jin abin a jikinmu ne! Saboda haka namu ne.

                “Ba ranar Juma’ar karshen Ramadan kawai ba, ko da wane lokaci muna tare da ‘yan Palasdinu, har izuwa tabbatan daulan Palastine a hannun Palasdinawa insha Allahul Azeem, wanda duk wani wanda zai zauna a muhallin nan, sai dai ya zauna a matsayin Bafalasdine, sawa’un shi Yahudu ne, ko Banasare, ko ma mene ne, amma Palasdinu kasar su ce ta gado, kuma su suke da hakkin su mallakin kasarsu, ba wani wanda ya isa ya je ya kafa musu kasa, ya ware yace wadannan daban ne, wadancan daban ne.

                “Kun ga Allah Ta’ala yadda ya tsine ma Fir’auna, yace: “Inna Fir’auna Ala fiyl Ard wa ja’alaha shiya’an yastad’ifu da’ifatan minhum yuzabbihuna abna’ahum wa yastahyi nisa’ahum, innahu kana minal mufsidin.” “Wa nuridu anna munna alal lazinas-tad’ifu fiyl ard wa naj’alahum a’immatan wa naj’alahumul warisiyn.” “Wa numakkina lahum fiyl ardi wa nuriya Fir’auna wa Hamana wa junudahuma minhum ma kanu yahzarun.”

                “To Fir’auna ya raba kasa, ya raunana wasu, ya daura wasu a kan wasu, yace wadannan sunansu Kibɗawa, wadannan sunansu Isra’iliyawa. Yana yanka ‘ya’ya maza na Isra’iliyawa. To Allah Ta’ala kuma yana son ya yi tagomashi ga wadanda ake zalunta, ya nuna wa Fir’auna da Hamana da rundunoninsu cewa wannan abin da suke gudu zai same su. Kuma abin da ya faru kenan, karshe sai da Allah Ya gusar da Fir’auna, da Hamana da mulkinsu, kuma Ya taimaki wanda ake zalunta.

                “To yanzu irin wannan ne zai faru, kuma wannan ayar ma da yawa masu fassara suna fassara “Wa nuridu anna munna alal lazinas-tad’ifu fiyl ard wa naj’alahum a’immatan wa naj’alahumul warisiyn.” Cewa da bayyanan Imam (AJ) ne. Cewa lokacin bayyanar Imam (AJ) insha Allah, wadanda ake zalunta Allah zai yi tagomashi gare su, ya nuna wa Fir’auna da Hamana, wanda su ramzi ne na duk azzalumai, wannan (lokacin) sai ya nuna ma Amerika da Birtaniya da ire-irensu abin da suke gudu. Insha Allahul Azeem wannan rana tana tafe. Muna fatan Allah Ta’ala ya gaggauta bayyanan wanda da bayyanansa ne za a samu mafita.”

Nakaltowa: Cibiyar Wallafa

25/Ramadan/1445

04/04/2024