Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

7 Faburairu 2024

07:29:58
1435942

A Irin Wannan Rana Ne Dai 26 Ga Watan Rajab Shekaru Goma Bayan Aiko Annabi SAWA Sayyid Abu Dalib AS Yayi Wafati

A yayin zagayowar ranar wafatin Abu Talib (a.s) na 26 ga watan Rajab.

Sunan sa Abdulmunaf dan Abdul Mudallib dan Hashim Mahaifi ga Imam Ali As kuma Baffa ga Annabin Rahama S wanda yabashi kariya da kulawa tundaga wafatin Babansa har zuwa lokacin da yayi wafati yak are shi daga dukka cutarwa ta Mushirikan labarawan Kuraishawa. Matarsa it ace fatimatu biint Asad Mahaifiyar dukan yayansa guda tara mata 5 4 maza.

An Haifeshi a shekaru 88 kafin Hijirar manzon Allah S shekaru 35 kafin Haihuwar Annabin SAWA.

                Yakasance madaukaki a cikin shugabannin mutanan Makka da Kuraishawa dama Bani Hashim gaba daya. Hamshakin dan kasuwa, Ya Rike matsayin Shaharwa da Masaukin  Dukkan mahajjata Kafin Aiko Annabi SAWA malaman tarihi sun kawo cewa ya kasance Shugaba ne da ake masa biyayya mai Kwarjini ne shi ga yawan Kyauta da Ciwarwa hatta kasance duk ranar da yake ciyawarwa ba wanda yak e ciyarwa a garin makka kamar yadda yake sannan kasancewar sa da danginsa suna kan Addinin Annabi Ibrahim As basu kauce a kansa ba shine wanda ya sunnata bayar da diyya ga iyalan wanda aka kashe kuma musulunci ya tabbatar da wannan hukunci nasa, ya haramtawa kansa shan giya kamar yadda yazo Sirah Halbiyyah.

                Kamar yadda kulawarsa ga Annabin rahama da gudunmawar da bayawar Addinin Allah a bayyane ya ke bayaninsa cikin littafan tarihi.

                Yayi wafati kwana 3 da wafatin Sayyidah Khadija a lokacin da yai wafati yana dan shekara 85 bayan zuwan labarin wafatinsa ga manzon Allah yayi bakinciki sosai inda Annabi yake cewa: Kuraishawa basu iya cimmani ba saida Abu dalib yayi wafati, bayan nan sai ga sakon Ubangiji tare da Jabra’il yana mai bawa Annabai umarni akan ya fita daga Makka saboda mai taimaka maka yayi wafati kamar yadda Annabi (SAWA) ya kira wannan shekarar da Shekara Bakinciki an binne shi a Makabartar Mu'alla ta Hujun.

Wannan hoton da kuke gani shine Makabartar Mu'alla ta Hujun makabartar Abu Talib tana a Makkah: kafin/da bayan rushewar da Wahabiyawa su kai mata.

Kabarin Sayyidina Abdul Muddalib da Abu Talib, a wata ruwayar da na Sayyida Amina da kuma Kabarin Sayyida Khadija, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su baki daya a wajen.

A yayin zagayowar ranar wafatin Abu Talib (a.s) na 26 ga watan Rajab.