10 Satumba 2023 - 08:36
Wani Matashin Bafalasdine Dan Shekaru 15 Yayi Shahada Bayan Yahudawan Sahyoniya Sun Harbe Shi

Majiyar labaran Falasdinu ta bayar da rahoton shahadar wani matashin Bafalasdine dan shekaru 15 da haifuwa a daren shekaran jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, a daren shekaran jiya Asabar ne majiyoyin labaran Falasdinawa suka bayar da rahoton cewa, yahudawan sahyuniya sun harbe wani matashi dan shekaru 15 a duniya.

Sunan wannan matashin "Milad Munzer al-Ra'i" wanda ya yi shahada sakamakon tsananin raunin da harbin Yahudawan sahayoniya su kai masa.

Ya kasance mazaunin sansanin al-Arub da ke arewacin Hebron, lokacin da ya ji rauni a rikicin da ya yi da yahudawan sahyoniya.

A 'yan sa'o'i da suka gabata Bayan aukuwar abun ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar da cewa an dauke wannan matashi zuwa asibitin Al-Imamah da ke sansanin al-Arub saboda tsananin raunin da ya samu.

Yahudawan sahyoniya sun kai masa hari a bayansa da kirjinsa, sannan kuma jami'an agajin agaji na Red Crescent na Palasdinawa suka kai shi asibitin Elimame da ke birnin Bethlehem saboda tsananin raunin da ya samu.

A makon da ya gabata ma a ranakun 30,31 ga watan ugusta da kuma 9, da 1 ga watan Satumba, wasu matasan Palastinawa 4 sun yi shahada a yankuna daban-daban Sakamakon harin Yahudawan.

Abdul Rahim Fayez Ghannam dan shekaru 36 da haifuwa, matashin Bafalasdine ne wanda ya samu raunuka kuma ya yi shahada a ranar 1 ga watan Satumba sakamakon raunukan da sojojin yahudawan sahyoniya suka yi masa a harin da suka kai yankin Tubas da ke yammacin gabar kogin Jordan a wannan rana.