Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

6 Satumba 2023

16:26:24
1391664

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Ku Yi Rayuwa Irinta Husaini, Ku Wanzu A Tafarkin Husain Idan Kuka Daure Zaku Kai Ga Gaci.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da irin yadda al'umma musamman matasa suka halarci tattakin Arba'in tun daga Najaf zuwa Karbala da ma sauran garuruwan kasar, inda ya yi magana zuwa ga matasa: Kamar yadda kuka yi tsayin daka a kan Muzaharar Tattakin Arba'in, to ku yi hakan kan kafuwar tafarkin Tauhidi, ku kasance masu karfi da azama, kuma a ko da yaushe ku rayu a Rayuwar Husaini, ku tabbata akan tafarkin Husaini.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake jaddada cewa matasa sune kololuwar fatan alheri ne, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da irin yadda al'umma musamman matasa suka halarci tattakin Arba'in tun daga Najaf zuwa Karbala da ma sauran garuruwan kasar, inda ya yi magana zuwa ga matasa: Kamar yadda kuka yi tsayin daka a kan Muzaharar Tattakin Arba'in, to ku yi hakan kan kafuwar tafarkin Tauhidi, ku kasance masu karfi da azama, kuma a ko da yaushe ku rayu a Rayuwar Husaini, ku tabbata akan tafarkin Husaini.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, an gudanar da zaman makoki a gaban Jagoran juyin juya halin Musulunci tare da halartar dimbin tawagogin dalibai a daidai lokacin da Arbaeen Husaini. A cikin wannan taro na juyayin shahadar Sayyid Aba Abdullah Husain (AS) da sahabbansa na hakika, an gudanar da waken Juyayi da kuma karanta Ziyarar Arbaeen.

A wannan taro Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Rostami shugaban Majlisin da ke wakiltar malaman fikihu a jami'o'i ya gabatar da jawabi inda ya bayyana sirrin dawwamammen waki'ar Karbala da kuma aikin Arba'in mai alfarma a wannan zamani da muke ciki.

A karshen wannan taron, an gudanar da sallar azahar da La'asar a karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci.

A cikin gajeren jawabin da ya yi a tsakanin salloli. biyu, Ayatullah Khamene'i ya kira kowane tarukan zaman makoki da kuma Tawassuli da Imam Husaini (a.s.) da cewa wata dama ce ta alaka da hasken ruhi da hasken da ba ya da iyaka na Husaini, ya kuma jaddada cewa muhimmin abu shi ne; kula da wannan alaka, kuma alaka tana tare da tafarki kai tsaye, wanda ke bukatar irada da juriya.

Ya yi nuni da cewa: Idan kuka daure kuka jure za ku iya kaiwa da galaba a kan kololuwar manufa, kuma za ku kai kololuwar samar da hukumar addinin Allah da mulkin gaskiya da adalci.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake jaddada cewa matasa abin fatan alheri ne, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da irin yadda al'umma musamman matasa suka halarci tattakin Arba'in tun daga Najaf zuwa Karbala da ma sauran garuruwan d birane kasar Iran, inda ya yi magana zuwa ga matasa: Kamar yadda kuka yi tsayin daka a kan Muzaharar Tattakin Arba'in, to ku yi hakan kan kafuwar tafarkin Tauhidi, ku kasance masu karfi da azama, kuma a ko da yaushe ku rayu a Rayuwar Husaini, ku tabbata akan tafarkin Husaini.