Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

7 Yuni 2023

12:54:53
1371646

Saudiyya: Gwamnatin Saudiyya Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Wasu Matasa 'Yan Shi'a 3

An yanke hukuncin kisa ga wasu matasa uku daga birnin Qatif na kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, majiyoyin yada labarai sun sanar da aiwatar da hukuncin kisa kan wasu ‘yan Shi’a matasa 3 daga birnin Qatif a gabashin kasar Saudiyya da gwamnatin Saudiyya ta yi.

A cewar rahoton, an zartar da hukuncin kisa kan wasu matasan Shi'a na Saudiyya "Husain bin Ali bin Muhammad Al-Mohishi" da "Fazli bin Zaki bin Husain Ansif" da "Zakariya bin Hasan bin Muhammad Al-Mohishi" wanda suna daga cikin matasan 'yan Shi'a na Saudiyya.


Gwamnatin Saudiyya ta zargi wadannan matasa da shiga kungiyar ta’addanci tare da mallakar makamai da horar da su, da kuma kai hare-hare da makamai kan cibiyoyin tsaro da nufin kashe jami’an tsaro.

Wannan gwamnatin ta yi barazana ga iyalan matasan da aka yankewa hukuncin cewa za a kama su idan suka yi magana game da 'ya'yansu ko kuma suka nemi a mayar da gawarwakinsu.

Yayin da ake aiwatar da hukuncin kisa kan wadannan matasa ‘yan Shi’a guda uku na Saudiyya, adadin matasan ‘yan Shi’a da gwamnatin Saudiyya ta kashe a cikin makonni biyu da suka gabata ya kai bakwai.

A kwanakin baya ne ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta sanar da aiwatar da hukuncin kisa kan wasu matasa 'yan Shi'a 'yan kasar Bahrain tare da bayyana cewa ana zargin wadannan mutane da kokarin haifar da rikici a kasashen Saudiyya da Bahrain.

Garuruwan da ke gabashin Saudiyya ‘yan Shi’a ne, kuma galibin mazaunan su ne gwamnatin Saudiyyan ke kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu saboda dalilai na siyasa.