Ministan da manyan manajoji na ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran da jakadu da shugabannin wakilan jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasashen waje sun gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci a safiyar yau (Asabar).
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, An gudanar da wannan taro ne a daidai lokacin da ake gudanar da taron shugabannin ofisoshin wakilan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasashen waje.