Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

8 Mayu 2023

02:18:06
1363611

Bayan shahadar Shaikh Khidir Adnan Al'ummar Bahrain Suna Neman A Kai Dauki Ga "Al-Sankiis"

A cikin makon nan ne masu fafutuka na kasar Bahrain suka tattauna kan batun shahadar shehin fursunoni "Shahid Khader Adnan" a yayin da yayi shahada bayan dogon tarihin gwagwarmaya, wajen kare kasar saboda fafutukar yanto Palastinu da kuma ganin andawo da hakkokin daga sahyoniyawan da suka kwace.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, masu fafutuka a kasar Bahrain sun alakanta shahidi "Khader Adnan" wanda ya yi shahada bayan yakin rashin ciki a cikin gidajen yarin mamayar, da kuma fursunonin lamiri Dr. Abdul Jalil Al-Singace" wanda ke yaki da rashin kin cin abinci a cikin gidajen yarin gwamnatin Bahrain .


A cikin makon nan ne masu fafutuka na kasar Bahrain suka tattauna kan batun shahadar shehin fursunoni "Shahid Khader Adnan" a yayin da ya shahada bayan dogon tarihin gwagwarmaya, masu kare kasar saboda fafutukar Palastinu da kuma dawo da hakkokin daga sahyoniyawan da suka kwace.


Shahidan yayi shahada ne bayan ya kwashe kwanaki 87 yana yaki kim cin abinci, saboda adawa da kama shi a gidajen yari na mamaya.


Labarin mutuwar fursunan "Khider Adnan" ya kasance kan gaba a shafukan sada zumunta a Bahrain, inda Al'ummar Baharain ke yada bidiyo da tweets da yawa.


Maudu'in "Khider Adnan Shahed" da "Bahrain_Al-Wefaq_Khader Adnan" na daga cikin wadanda suka fi shahara da yaduwa a shafukan sada zumunta a Bahrain.


Masu fafutuka na Bahrain sun danganta mutuwar fursuna Khader Adnan da fursunan lamiri a Bahrain, karkashin jagorancin Dr. Abduljalil Al-Singace, wani marubuci kuma mai fafutukar kare hakkin bil adama, wanda ya shafe kwanaki sama da 600 na yajin cin abinci a gidajen yarin gwamnatin Bahrain. .

......................