Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

27 Janairu 2023

10:20:06
1341314

Ayatullah Ramezani: Ya kamata tsare-tsare da ayyukan kamfanin dillancin labarai na Abna su kasance daidai Cikin Sauyi.

Sakatare Janar na Majalisar Duniya taa Ahlul-Bait (AS) ya ziyarci sassa daban-daban na Kamfanin Dillancin Labarai na Abna a lokacin da ya halarci ofishin Kamfanin Dillancin Labarai na Abna.

Kamfanin dillancin labaran *ABNA24* ya habarta cewa, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (AS) ya ziyarci sassa daban-daban na kamfanin dillancin labarai na Abna a lokacin da ya halartaci ofishin kamfanin dillancin labarai na Abna.

Ayatullah "Riza Ramizani" ya jaddada batu dangane cudanya da mu'amala da shafukan labarai, inda ya ci gaba da cewa: Hanya ta mu'amala tana da matukar muhimmanci a cikin ayyukan kamfanin dillancin labarai na Abna, wanda ya kamata ya zamo an yi amfani da dandali ta hanyar da ya dace domin nuna ayyukan 'yan Shi'a, a kasashe daban-daban."

Ya yi nuni da wajibcin ayyukan ‘yan jarida abun karramawa ya kara da cewa: kamata ya yi a tsara shi ta yadda ‘yan jarida masu karramawa za su yi aiki mai karfi. A ƙasashe daban-daban, mutane da yawa za su iya ba da haɗin kai ga Abna bisa ga girmamawa, kuma 'yan jarida masu daraja za su iya mayar da Abna kamfanin dillancin labarai na musamman.

Ana yawan kawo ziyara Abna kuma masu sauraro sun amince da dandalin.

Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya bayyana cewa kwararru da Ma'aikata masu addini suna aiki a Abna, inda ce: Abna kamfanin dillancin labarai ne na kasa da kasa, kuma ya kamata ya kara yin la'akari da lamuran duniya.

Ƙaddamar da samar da ƙarin labarai, ƙarfafa harsuna, wajibcin zama tushen labarai ga sauran kamfanonin labarai, yin amfani da Dabaru, hikima da ƙoƙari na gamayya, wajibcin yin hira da mutane da dattawa, da tsarawa na gajeren lokaci da dogon lokaci; na daga cikin Shawarwari na babban sakataren majalisar duniya na Ahlul-Baiti (AS) na cikin wannan ziyara inda ya kara da cewa tsare-tsare da ayyukan Abna su kasance daidai da Samun sauyi.

A yayin wannan ziyarar, Hassan Sadraei Aref, shugaban kamfanin dillancin labarai na Abna, ya yi bayani kan ayyukan wannan kamfanin dillancin labarai da shirye-shirye masu zuwa, sannan ya gabatar da rahoton ayyukan Abna a baje kolin "Anwar Hedayat" ga babban sakataren majalisar duniya Ahlul Baiti (AS).

Idan dai ba a manta ba, a wannan ziyara, Injiniya Ghulamreza Sharifi, babban daraktan fadar shugaban kasa ta majalisar duniya ta Ahlul-Baiti (AS) shine yayi rakiya ga Ayatullah Ramezani.